’Yan bindiga da ake zargin yaran fitaccen jagoran ’yan bindiga Bello Turji ne, sun ƙwace yankin Bafarawa, garin su tsohon gwamna Attahiru Dalhatu Bafarawa.
’Yan bindigar sun kai harin tare da ƙwace wasu ƙauyuka huɗu ne a ranar Asabar a Ƙaramar Hukumar Isa ta Jihar Sakkwato.
Harin, wanda ake zargin wani kwamandan Turji mai suna Danbakolo ne ya jagoranta, ya kuma shafi ƙauyukan Gebe, Kamarawa, Garin Fadama da Haruwai.
Ana zargin harin da aka kai da kusan ƙarfe 11 na safe ran Asabar, martani ne ga ayyukan sojoji na baya-bayan nan da suka yi niyyar fatattakar ’yan bindiga a yankin.
- NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Tasirin Amfani Da Irin Noma Na GMO
- NDLEA ta kama matar da ta ɓoye hodar iblis a al’aurarta
Majiyoyi a yankin sun ce an kashe mutane uku—ciki har da wata mata da ɗanta—a lokacin harin, wanda wasu mazauna ke zargin na hannun Turji ne ya jagoranta.
Maharan sun yi wa Bafarawa ƙofar rago, inda suka zargi mazauna da bai wa sojoji bayanan sirri.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilinmu cewa maharan, “Sun tafi kai tsaye fadar Sarkin Gabas na Bafarawa, Alhaji Muhammad Dalhatu, wanda shi ne babban ɗan uwan tsohon gwamnan.
“Sun yi ta neman sa, sun tafi da kuɗinsa da wayoyinsa, kuma sun yi wa al’umma gargadi game da haɗa kai da jami’an tsaro.”
Mazauna ƙauyukan da abin ya shafa sun gudu zuwa garin Shinkafi da ke kusa domin tsira.
Sai dai rahotanni sun ce sojoji sun ƙarfafa musu gwiwa da su koma gida a ranar Lahadi, tare da ba su tabbacin ingantaccen tsaro.
Lokacin da aka tuntube shi domin jin ta bakinsa, kakakin ’yan sanda na Jihar Sakkwato, DSP Ahmad Rufa’i, ya musanta faruwar lamarin.
Ya ce, “Ba na tunanin akwai wani abu kamar haka saboda akwai jami’an tsaro da yawa a waɗannan yankunan.”
Duk da musantawar, majiyoyi da yawa sun tabbatar da cewa hare-haren sun faru kuma sun bar mazauna cikin tsoro.