Gwamnatin Jihar Katsina ta ce yara kimamin 775,000 ne suka daina zuwa makaranta saboda matsalar rashin tsaro a jihar.
Daraktan Hukumar Kula da Ilimin Bai-daya a Matakin Farko (SUBEB) ta jihar, Abdulmalik Bello, ya ce shekarar 2018 kadai, yara miliyan daya da dubu 137 ne suka bar zuwa makaranta a Jihar Katsina.
- ’Yan sa kai sun kashe liman yana sallah da wasu mutum 10 a Sakkwato
- Ba cin bashi ba ne babbar matsalar Najeriya – Ministar Kudi
“Idan aka yi la’akari da sakamakon kidaya da ake yi duk shekara a makarantu, yanzu muna da yara fiye da 775,000 da suka bar makaranta,” kamar yadda ya bayyana.
Ya kara da cewa daga cikin yaran da suka daina zuwa makaranta, an yi kokari 360,000 sun koma, da taimakon gwamnatin jihar da hadin gwiwar Asusun Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) da hukumar kula da ilimi a matakin farko ta kasa.
Bello ya shaida wa wani gangami da aka shirya kan komawa makaranta a jihar cewa matsalar daina zuwa makarantar yara a jihar ta fi kamari kananan hukumomin Kankara da Kafur.
Ya bayyana cewa hare-haren ’yan bindiga da cutar COVID-19 su ne manyan ummulhaba’isin daina zuwa makaranta da yara ke yi a jihar.
An gudanar da taron ne a ranar Laraba da hadin gwiwar UNICEF da kuma Ofishin Kula da Ci gaban Kasashe Rainon Ingila (FCDO).
-
– Rashin tsaro a Jihar Katsina
Jihar Katsina ta na ci gaba da fama da matsalar tsaro da ke yin sanadiyyar salwantar rayuka da dukiyoyi, baya ga raba mutane da muhallansu.
A lokuta da dama mahara sun kai hari a makarantun boko da na Islamiyya a jihar inda suka yi awon gaba da dalibai masu yawan gaske kafin daga baya a sako su.
Al’ummomi da dama sun tsere sun bar garuruwansu da gonakinsu, a sakamakon hare-haren ’yan bindiga da a wasu lokuta sukan yi wa mata fyade ko su kona gidaje su kuma yi awon gaba da dabbobin jama’a.