✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yara 545,000 ba sa zuwa makaranta a Adamawa —UNICEF

Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya akalla yara 544,951 marasa zuwa makaranta a Jihar Adamawa a shekara ta 2019. Babban Jami’in…

Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya akalla yara 544,951 marasa zuwa makaranta a Jihar Adamawa a shekara ta 2019.

Babban Jami’in Binciken na Ofishin Hukumar a Najeriya, Mista Bhanu Pathak shi ne ya tabbatar da hakan yayin wani bikin fara gini da kuma gyaran makarantu 80 a jihar da ya gudana a Karamar Hukumar Fufure ranar Alhamis.

Sai dai ya ce bayan hobbasan da hukumar da hadin gwiwar gwamnatin jihar, fiye da kaso 94 cikin 100 na yaran sun koma makaranta.

A cewarsa, “Daya daga cikin irin nasarorin da muka samu shi ne mun gano yara kimanin 544,951 a kananan hukumomi biyar na Adamawa inda muka samu nasarar mayar da kashi 94 cikin 100 na yaran zuwa makarantun.

“Yau kuma ga shi muna shaida sake kaddamar da wani shiri na ginawa da kuma gyara makarantu 80 kafin karshen 2020”, inji Bhanu.

Jami’in ya kuma ce nan ba da jimawa ba za a sake daukar wasu karin makarantun da kuma suke fatan zai inganta harkar ilimi a jihar.

Bhanu ya kuma ce gwamnatin kasar Jamus da UNICEF ne suke daukar nauyin gyaran.

Ya kuma yaba wa gwamnatin jihar saboda bayar da gudunmuwar Naira miliyan 200 domin tabbatar shirin.

Gwamnan jihar, Ahmad Umar Fintiri ya yaba wa hukumar a kokarin da take yi na ganin dukkannin yaran jihar suna zuwa makaranta, wanda ya ce shirin ya zo daidai da kudurin gwamnatinsa.

“Ina matukar farin ciki da irin cigaban da aka samu, ina godiya ga UNICEF da sauran kungiyoyi masu ba da tallafi na daukar nauyin wadannan shirye-shiryen.

“Ina kira ga iyaye da sauran shugabannin al’umma kan su tabbatar yara suna ci gaba da zuwa makaranta da zarar an koma”, inji gwamna Fintiri.