Duk wanda ya yi makarantar kwana a shekarun baya ba zai manta irin horon da ake samu a tsakanin dalibai ba.
Irin wannan horon ne mutane da dama a yau suke kallonsa a matsayin zalunci; yayin da a baya mutane da dama ke daukarsa a matsayin wani abu na saita tarbiyyar dalibai.
- Hausawa ’yan APC sun tsallake rijiya da baya a ranar zaɓe a Ibadan
- Yadda waƙar Rarara ta ɗaga darajar Fatima Mai Zogale
Duk da cewa wadansu daliban kan wuce gona-da-iri wajen bayar da horon, wasu na ganin idan aka dubi ainihi da kuma tsarin al’amarin za a ga ya samo asali ne daga bayar da tarbiyya da ke nuna cewa dole na kasa ya yi wa na sama da shi biyayya.
Salon wannan horon za a iya kasa shi kashi-kashi; akwai horo na biyayya akwai horo na aikata laifi, sannan akwai na cin zali.
Idan ba a manta, a makon jiya Aminiya ta ruwaito yadda aka rufe makarantar Lead British International da ke Abuja bayan yaduwar bidiyon wasu daliban makarantar sakandaren suna ci zalin dayarsu.
A cikin bidiyon da ya karade kafofin sada zumunta an ga wasu daliban makarantar mata su biyu suna marin wata daliba.
A gefensu kuma wani dalibi namiji yana dariya, a yayin da daliban suke marin nata, ita kuma babu abin da ta yi.
Sai daga baya an dauki mataki, inda dalibar wadda ta yi marin ta fito a wani bidiyo tana neman afuwar kuskuren da ta yi.
Wannan lamarin ne ya jawo ce-ce-ku-ce a kafofin sadarwa, inda mutane da dama suka fara waiwaye tare da bayyana irin horon da suka fuskanta a baya.
A daidai lokacin da ake tafka muhawara a kan lamarin, Aminiya ta lura an samu sabanin fahimta; inda wasu ke ganin ya kamata a kawar da irin wannan horo a makarantu, wasu kuma ke ganin horo a makaranta na gyara tarbiyya.
Masu ganin horo a kan laifi kan sa dalibai su ji tsoro su yi kokarin guje wa aikata laifuffuka don kauce wa irin wannan horo.
Kuma yawancin wannan horo shugabannin dalibai da ake kira prefect ne suke aiwatar da shi ga dalibin da ya aikata laifi.
Misali laifin kin yin sharar dakunan kwana ko wankin bandakunansu. Kuma idan aka dauki horo na biyayya irin wanda ke gudana a tsakanin daliban da ake babban aji da na kasa, misali dan aji daya dole ya yi biyayya ga dan aji biyu haka shi ma dan aji biyu zai irin wannan biyayyar ga dan aji uku, haka abin yake har zuwa sama.
Kuma yawancin irin wanan horon yakan hada da aiken dalibi ya debo ruwa ko ya karbo wani sako a wurin wasu ko ya sayo wani abu a kantin makaranta, a wasu wuraren ma akan ba daliban wankin kaya da sauransu, ya danganta da makarantar.
To sai dai kuma idan aka samu dalibin ya ki yin biyayya ga dalibin da ke sama da shi to wannan dalibi yana da damar yi wa dalibin horo bisa laifin da ya aikata masa.
‘Irin horon da muka sha a makaranta’
Malama A’isha Yunusa wata malama ce da ta ce ta yi makarantar kwana shekara 35 da suka gabata, inda ta bayyana cewa a yanzu irin wannan horo ba zai yiwu a kamarantun kwana ba, saboda yaran ba irin na da ba ne, don haka ba za su yarda a yi musu wannan horo ba.
“A gaskiya ba na zaton ’ya’yanmu za su yarda a yi musu irin wannan horo da aka yi mana. Saboda idan kin duba ’ya’yan yanzu ba irinmu ne ba.
“Wadanda muka tashi da tsoro da kunya da kuma biyayya, ’ya’yan yanzu iyayensu ma sai sun bi a sannu idan ba haka ba, kuwa sai a zo na jin kansu, ballantana dalibai da suke kallon kusan kansu daya.
“Ina iya tunawa akwai wasu dalibai da suke sama da mu, mu ne muke yi musu wankin kayansu, mu ne muke karbo musu abinci a dakin cin abinci.
“Kai muna yi musu abubuwa da dama. Amma a gaskiya mu suna kula da al’amuranmu domin idan ba mu da lafiya su ne suke tsayawa a kanmu har sai mun warke ta hanyar kai mu ga hukumar makaranta don kai mu asibiti da sauransu.
“Kuma ba su yarda wasu daliban su rika wahalar da mu,” in ji ta.
Shi ma Garba Sani wanda ya ce ya yi makarantar kwana a shekarun baya, ya ce duk da cewa a wancan lokaci suna kallon horon a matsayin zalunci, yanzu ya fahimci cewa ana yin sa ne da nufin yi wa yara tarbiyya.
Ya ce, “An yi mana ne don mu samu tarbiyya kuma wallahi wannan abin ya taimaka mana a rayuwa, domin a lokacin manyanmu sun daidaita mana sahu ta yadda muka koyi hakuri da yin biyayya ga na gaba.”
Ita ma wata malama mai suna Binta Umar ta ce horon da ake yi a tsakanin dalibai na sanya yara ko dalibai su san kimar iyayensu tare da girmama su.
A cewarta irin wancan horon yana da amfani musamman yana saita mutum, ya zama ya koyi tafiyar da rayuwarsa bisa tsari “Wallahi wannan horon da ake yi wa dalibai ya sa dalibai da yawa sun natsu sun shiga taitayinsu sun san darajar iyayensu.
Musamman irin ’ya’yan da suka zo makaranta a sangarce wadanda tun farko za ki ga iyayen ba su isa da su ba.
Amma idan suka zo makarantar kwana suka ga yadda ’yan uwansu dalibai suke horar da su, sai ki ga idan sun koma gida hutu iyayensu suna ganin bambancin natsuwar da dansu ya samu a makaranta.
Wannan kuwa ba komai ba ne illa ji da yaron ya yi a jikinsa. Ni a yanzu na yafe wa duk wacce ta yi min wani horo a makaranta kasancewar na fahimci alfanunsa,” in ji ta.
Yayin da take goyon bayan abin da Malama Binta ta fadi Malama Khadija Ali ta ce horon da ake samu yana taimaka wa dalibai su samu gogewa ta rayuwa.
“Za ki ga misali mu da muka je makarantar kwana ko iya wanki ba mu yi ba, saboda a wancan lokacin duk wasu ayyuka masu wahala ba a sanya mu yi a gida.
Amma da muka je makarantar kwana sai ya zama mu ne muke yi wa kanmu komai har da debo ruwa daga wani wuri mai nisa saboda a lokacin ana matukar wahalar ruwa.
Bayan mun debo namu mukan kuma debo na wasu daliban da ke gabanmu. Abubuwa da dama sun sa mun samu darasin rayuwa kuma har yanzu muna ganin amfaninsa ko in ce yana yi mana tasiri a rayuwa,” in ji ta.
Sai dai abin ba haka yake ga Malama Khadija Muhamamd Tukur ba domin a cewarta horon da ake bayar wa a tsakanin dalibai akwai na’uin zalunci da rashin imani a ciki.
Ta ce, “Ni ma ba na musun cewa an fito da tsarin ne da manufa mai kyau, sai dai daliban wanacan lokaci sun mayar da shi zalunci domin abin da suke yi malamin da ya san daraja da ciwon ’ya’ya ba zai yi ba.
Sai fa a lokaci guda a aiki dalibi wurare daban -daban kusan sau biyar ba tare da tausaya masa ba.
Kuma su babu ruwansu ko mutum ya ci abinci ko bai ci ba. Ko ya yi wanka ko bai yi ba in dai bukatarsu za ta biya shi ke nan. Kin san dai iyaye ba za su yi haka ba.
Ni fa a makarantarmu na san wasu daliban da suke sanya wasu daliban su yi musu tausa da sauransu.”
Bayan wannan, Aminiya ta lura da wasu da suka shiga Facebook suka bayyana yadda suka sha wahala daban-daban, inda wasu suka bayyana yadda aka rika yi musu dukan kawo wuka.
Akwai wanda ya ce an masa mari ya fi 50 a fuska, wani kuma bulala sama da 50 ya ce an yi masa da sauransu, wadanda duka irin wannan horo sun saba da ka’idar horo a doka da hankali.
Haka lamarin yake a makarantun allo, inda manyan almajirai sukan tura kananan su je su yi bara, idan sun samo abinci mai dadi su kawo musu, idan kuma ba haka, suna fuskantar barazanar bulala.
Abin da masani ya ce
Dokta Sani Adamu kwarare ne a bangaren ilimi kuma malami ne a Jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Jihar Kano ya bayyana irin wannan horo a matsayin wani abu da ke saita rayuwar dalibai wajen fuskantar kalubalen rayuwa da ke gabansu.
Ya ce, “Duk da cewa a bangaren ilimi babu irin wannan horo, sai dai idan an dubi a inihin manufar lamarin za a ga cewa abu ne mai kyau, domin yana saita rayuwar dalibai.
A wannan lokaci kusan yara sun zo daga wurare dabandaban kuma idan aka duba yawanci a wancan lokaci yaran suka fara barin gaban iyayensu, kuma a wannan lokaci za su zauna ne a kan kansu, don haka suna bukatar wanda zai saita rayuwarsu don su zama masu hankali a cikin al’umma.
“Ita makarantar kwana ma gaba daya wuri ne da yaro ko dalibi ke samun tarbiyyar rayuwa ta kowace fuska. A can yake koyon hakuri da iya zama da jama’a.
“Misali idan muka dauki bangaren abinci za mu ga cewa a makarantar kwana yaro yakan ci kowane irin abinci ba tare da zabi ba da sauransu,” in ji shi.
Sai dai ya yi kira ga hukumomin da ke da alhakin kula da irin wadannan makarantu da su rika sa ido a taskanin daliban don ka a yi amfani da irin wannan horo a cutar da daliban.