✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yar shekara 92 ta kafa tarihi a tseren fanfalaki

Wata tsohuwa ’yar kimanin shekara 92 wadda ta farfado daga ciwon kansa mai suna Harriette Thompson ta kafa sabon tarihi a gasar gudun fanfalaki (Marathon)…

Wata tsohuwa ’yar kimanin shekara 92 wadda ta farfado daga ciwon kansa mai suna Harriette Thompson ta kafa sabon tarihi a gasar gudun fanfalaki (Marathon) a ranar Lahadin da ta gabata a Amurka. Tsohuwar ta kafa sabon tarihin ne bayan ta shafe kimanin awa 7 da minti 24 da dakika 36 tana sheka gudu ba tare da ta gaji ba, hasalima a karshe ita ce ta zama zakara.

Harriette Thompson dai tana zaune ne a Charlotte da ke Kudancin Carolina na Amurka. Ta fafata ne a gasar tseren gudun fanfalaki da wani kamfani mai suna Rock ‘n’ Roll na Amurka yake shiryawa a duk shekara a garin San Deigo.
Jim kadan bayan ta kai layin karshe da aka zana na wadanda suka zama zakara ne magoya bayanta da ’yan uwa da abokan arziki suka rika tsalle suna murnar nasarar da ta samu.
Kamfanin watsa labarai na Associate Prees wanda ya ruwaito labarin ya ce tsohuwar ta nuna matukar farin cikinta da kuma godiya a bisa wannan nasara da ta samu. “A gaskiya na yi murna musamman ganin yadda magoya bayana suka rika murna suna kiran sunana inda nan take filin ya rude ba ka jin komai sai yabo na da ake yi kuma hakan ya karfafa min gwiwa matuka”, inji ta.
Ta ce duk da matsalar da ta samu a baya, a lokacin da maigidanta yake kwance bai da lafiya inda ta dauki tsawon lokaci ba tare da ta yi atisaye ba, daga baya ne maigidanta ya rasu a watan Janairu amma tana shirin fara yin atisaye ne kuma sai ta ji rauni a kafa.. Daga nan ne ta cigaba da jinyar raunin al’amarin da ya sa ba ta samu sauki ba sai ana gab da fara wannan gasa. Ta ce ba tare da bata lokaci ba ta shiga gasar, kuma ga shi Allah Ya ba ta nasara inda ta zama zakara a gasar.
Wadanda suka shirya gasar sun ce tsohuwar mai kimanin shekara 92 da kwanaki 65 a duk shekara tana halartar wannan gasa da suke shiryawa, hasalima yanzu ta kafa tarihi a matsayin tsohuwar da ta fi yawan shekaru wacce ta zama zakara a bana.
Sai dai an taba samun wata tsohuwa mai suna Gladys Burill ’yar kimanin shekara 92 da ta fito daga yankin Ingila wacce ta fafata a gasar da kamfanin Rock ‘n’ Roll ya shirya ita ma ta taba fafatawa a gasar a shekarar 2010 a Amurka a tseren da ake kira Honolulu Marathon. Sai dai Gladys ba ta kai zagayen karshe a gasar ba ta sare inda ta fadi kasa warwas kuma aka kai mata agajin gaggawa.