✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yar shekara 15 ta kashe kanta a Jigawa

Wata yarinya ta kashe kanta a unuguwar Kofar Gabas da ke karamar hukumar Gwaram a jihar Jigawa. Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Jigawa Abdu…

Wata yarinya ta kashe kanta a unuguwar Kofar Gabas da ke karamar hukumar Gwaram a jihar Jigawa.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Jigawa Abdu Jinjiri, wanda ya tabbatar da hakan ga manema labarai ranar Laraba, ya ce yarinyar ta hallaka kanta ne ta hanyar shan maganin kwari.

“Ranar 4 ga watan Afrilu da misalin karfe 5 na yamma aka kai wa ’yan sanda a karamar hukumar Gwaram rahoto cewa wata yarinya ’yar shekara 15 mai suna Ummi Garba ta sha gubar “Sniper” ta fadi magashiyyan.

“’Yan sanda sun ruga da ita asibiti, amma ana zuwa likitoci suka tabbatar da cewa ta cika”, inji SP Jinjiri.

Babu cikakken bayani game da dalilin yarinyar na shan guba, amma a cewar kakakin na ’yan sanda, bincike ya nuna cewa yarinyar ta ce ta gaji da rayuwa.

Sai dai bai fadi abin da ya sa ta ce ta gajin ba.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya kuma ambato SP Abdu Jinjiri yana cewa ana ci gaba da bincike.

 

%d bloggers like this: