✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yar shekara 110 ta shiga makaranta a Saudiyya

Wata dattijuwa mai shekaru 110 a kasar Saudiyya,  Nawda Al-Qahtani, ta shiga makaranta domin yaki da jahilci.

Wata dattijuwa mai shekaru 110 a kasar Saudiyya,  Nawda Al-Qahtani, ta shiga makaranta domin yaki da jahilci.

Malama Nawda mai ’ya’ya hudu, wanda babbansu ke da shekaru 80 dan autan kuma shekaru 50, ta ce ba ta taɓa fashi ba tun da ta fara makarantar.

Hakazalika ba ta wasa da duk aikin gida da malamai suka bayar a makarantar, inda ita da takwarorinta masu manyan shekaru suke koyon hada baƙi da kuma karatu Al-Kur’anin.

Ɗalibai masu kowane irin shekaru na halartar makarantar mai suna Al-Rahwa da ke yankin Umwah.

Dattijuwa Nawda ta kara da cewa ta jima tana son shiga makaranta, amma sai yanzu ta yunƙura ta yi a aikace.

Ta danganta rashin komawarta makaranta da yanayin yankunansu na karkara inda ’ya’ya mata ba sa samun damar kammala karatu.

Dattijuwar ta yaba wa gwamnatin Saudiyya bisa ƙoƙarinta na kawar da jahilci a ƙasar, inda ta ce da tun da daɗewa ta koma makaranta, ta tabbata da hakan ya matuƙar inganta rayuwarta da na sauran mutane irinta.

Amma duk da haka ’ya’yanta na  goyon bayan komawarta makaranta, inda suke bata ƙwarin gwiwa da kuma kyakkyawan fata. Sun kuma  bayyana rashin komawarta makaranta tun a baya a matsayin ƙaddara.

Danta Mohammed mai shekara 60, wanda kullum yake kai ta makarantar da safe, kuma ya jira har a tashi ya dawo da ita gida, ya bayyana farin ciki da cewa kullum mahaifiyarsa tana koyon sabon abu.

“Mun san wannan ba abu mai sauki ba ne ga mahaifiyarmu mai shekara 110, amma abun alheri ne kuma duk danginmu na alfahari da hakan.

“Da abin da za mu iya ne, da tun tana matashiya mun sama mata ingantaccen ilimi,” in ji Mohammed.

Kasancewar makarantar sakandaren ’yan mata ɗaya ce a yankin, ya yi kira ga gwamnati ta ƙara samar da ƙarin wasu, domin rage nauyin da ke kan makarantar ita kaɗai.

Hakazalika ya buƙaci gwamnati ta samar da ƙarin makarantun firamare domin tabbatar da cewa ƙananan yara ba su taso cikin jahilci ba, sannan su samu damar kammala karatunsu.

Ya yi kira ga gwamnatin yankin ta yi duk abin da ya kamata na kawar da jahilci domin inganta rayuwar mazauna da matasa su yi gogayya da takwarorinsu a kowane fanni.