Wani abin mamaki a kasar Sin shi ne wata tsohuwa mai shekara 109 ta himmatu wajen aikin gona a garinsu na Chongking. Jaridar Chongking Commercial Daily ta ruwaito labarin Zheng Shiding, wadda ke zaune a gundumar Tongnan, kuma an haifeta a shekarar 1908, inda a ranar 31 ga watan Yuli ta cika shekara 109.
Dattijuwa Zheng na zaune ne tare da ’ya’yanta 28 da jikoki da sauran iyalanta. In an tattara iyalan wannan tsohuwa za a samu mataki biyar na iyaye da ’ya’ya da jikoki. ’Ya’ya da jikokin Zheng sun yi ta kokarin ganin ta zauna ta huta, har ma nuni suka yi mata kan cewa ta kyale matasa su yi aikin gona. Duk wannan kiran na iyalan Zheng ta ci gaba da fafata aiki a gona a boye.
“Har yanzu ina da kuzarti da koshin lafiya. Zan ji babu dadi idan na zauna ba na aikin komai,” inji ta.
“Mahaifiyata ba ta taba zama ba ta aikin komai ba. Ta yi aiki tukuru tsawon rayuwarta,” a cewar Ji Shengyan, dan Zheng mai shekara 73. A cewar Ji, Zheng har yanzu tana taimaka wa wajen girbin kabewa da yi wa shuka ciro, ta yi wanke-wanke da sauran ayyuka. “Har ma aikin gona ta yi a zagayowar ranar haihuwarta,” inji Ji.
Ji ya bayyanha wa manema labarai cewa, Zheng na jin dadin kallon talabijin, musamman idan ana nuna Kung Fu da yake-yake. A wasu lokuta ta kan dade tana kallon shirye-shiryen da ta fi so har zuwa tsakar dare.
Shi kuwa Gwamnan garinsu cewa ya yi a daukacin fadin garin akwai masu shekara 100 su hudu, kuma Zheng ce ta fi su tsufa.
’Yar shekara 109 na fafata aikin gona
Wani abin mamaki a kasar Sin shi ne wata tsohuwa mai shekara 109 ta himmatu wajen aikin gona a garinsu na Chongking. Jaridar Chongking Commercial…