✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yar Sarkin Kano Muhammad Sanusi I ta rasu

Allah Ya yi wa daya daga cikin ’ya’yan Sarkin Kano na 11,  Muhammadu Sunusi I rasuwa. Gidan rediyon Freedom da ke Kano ya ruwait rasuwar…

Allah Ya yi wa daya daga cikin ’ya’yan Sarkin Kano na 11,  Muhammadu Sunusi I rasuwa.

Gidan rediyon Freedom da ke Kano ya ruwait rasuwar Hajiya Hadiza Sunusi waddda aka fi sani da Fualnin Gandu, ta daga daya daga cikin surukanta, Sa’adatu Baba Ahmad.

Fulanin Gandu ta rasu ne ranar  Alhamis 21 ga Janairu ana kuam sa ran yin jana’izarta a Kofar Kudu, Fadar Sarkin Kano da la’asar.

Fulanin Gandu ’yar uwa ce ga mahaifin tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.