Fatima Ganduje Ajimobi, diyar Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ta caccaki gwamnati kan harbin masu zanga-zanga #EndSARS da sojoji suka yi.
Kimanin mako biyu ke nan bayan mahaifinta, Abdullahi Gaduje ya dakatar da Hadiminsa, Salihu Tanko Yakasai, saboda sukar Gwamantin Shugaba Buhari a kan yin watsi da zanga-zangar #EndSARS.
- Fatima Ganduje ta sharwaci masu zanga-zangar #ENDSARS
- EndSARS: An fara binciken harbin da ka yi a Lekki
- Babu wanda aka kashe a harbin Lekki —Gwamnan Legas
Amma a sakon da ta wallafa a shafinta an Instagram Fatima ta ce, “ina matukaar bakin cikin goyon bayan da na yi wa wadannan shugabannin marasa tausayi”.
Ta wallafa sakon ne awanni kadan bayan harbin da sojoji suka yi domin watsa masu zanga-zangar #EndSARS a Lekki, Jihar Legas.
Diyar Gwamnan Kanon ta ce takan shiga rudu a duk lokacin da ta tuna cewa ta goyi bayan wannan gwamnati a baya, kamar yadda ta wallafa a shafin Instagram.
Ta kara da cewa a matsayinta na ‘yar Najeriya kasar ce a gabanta don haka babu abin da zai hana ta tsokaci kan abun da ba ya tafiya daidai.
Wannan ba shi ne karo na farko da diyar gwamnan ta yi tsokaci ta kafar sada zumunta kan abubuwa ba.
Kamar sauran lokuta, a wannan karon ma kalaman na dan diyar Gwamna Ganduja sun jawo ce-ce-ku-ce.
Wasu daga cikin wanda suka tofa albarkacin bakinsu, na ganin cewa abin da ta yi daidai ne, wasu kuma na ganin ba huruminta ba ne, duba da yanayin da kasar ta tsinci kanta.
Sai dai wasu fusatattu sun maida mata da martani, inda suka zarge ta da shiga harkokin siyasa, wanda ba shi ne karo na farko da hakan ta taba faruwa ba.