Wani magidanci ya bayyana wa Kwamatin Karbar Korafe-korafen wadanda zanga-zangar EndSARS ta ritsa da su a Jihar Edo, yadda ya rasa matarsa sakamakon tsare shi da ’yan sanda suka yi ba bisa ka’ida ba.
Mista Agbontaen ya ce ’yan sanda sun tsare shi ba bisa ka’ida ba kan wata takardar zarge-zarge da suka rubuta a kansa.
- Sace dalibai: Ya kamata gwamnati ta muttsuke ’yan ta’adda
- COVID-19: Najeriya za ta ci tarar masu kin sa takunkumi N20,000
- Sabbin ma’aikata 774,000 za su fara aiki ranar 5 ga Janairu, 2021 —Minista
Agbontaen ya bukaci a biya shi diyyar ran matarsa, sannan ya ce ya rasa komai nasa a sakamakon tsare shin da aka yi ba bisa ka’ida ba.
“Ina gida da misalin karfe biyu na dare kwatsam sai jin shigowar wasu ’yan sanda na yi cikin gidana suna kwankwasa kofa; saboda rashin bude musu kofar da wuri suka balle ta suka fara duka na.
Ya ce: “’Yan sandan sun kai ni caji ofis dinsu inda na bar matata da tsohon cikin wata takwas a gida, na kwashe mako biyu a tsare kafin a kai ni gidan yari.
“Ina gidan yari ’yan uwana suka sanar da ni an kwanatar da ita asibiti za a yi mata aikin fito da jariri da take dauke da shi (CS), bayan kwana 10 sai kuma suka sanar da ni ta rasu.
“Bayan an gama bincike a Sashen Binciken Manyan Laifuka sai jami’in dan sanda mai binciken ya ce babu tuhumar da zan amsa.
“Na ci gaba da zama a gidan yari, duk da na rasa matata; gonata da na bari cike da dawa na dawo na tarar wuta ta babbake ta. A takaice dai na rasa komai nawa.
“Wadannan dalilan ne suka sa na yanke shawarar bayyana a gaban wannan kwamatin saboda a biya ni diyyar asarar da na yi, wanda da ba a tsare ni ba da akalla zan samu damar taimakon matata”, inji shi.