Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi karin albashi ga ma’aikata da nufin rage musu radadin cire tallafin mai.
Tinubu ya ce karin albashin na wucin gadi ne kuma an tsara shi ne ta yadda ba zai haddasa hauhawar farashin kayan masarufi ba.
- Najeriya@63: Barnar da rashin shugabanci nagari ya yi
- Uwa ta kama wanda ya yi garkuwa da ’yarta a wajen karbar fansa a Zariya
Wannan na da daga cikin abubwan da shugaban kasar ya fada a jawabinsa ga ’yan Najeriya na cikar kasar shekakara 63 da suman ’yancin kai.
Ga abubuwan da ya fada jawabin na safiyar Lahadi a takaice:
1- Karin albashi
Tinubu ya sanar cewa “karamin ma’aikaci zai samu karin N25,000 a kan albashinsa a wata shida masu zuwa.”
Sai dai bai yi karin haske kan abin da karin ya kunsa ba ko lokacin da za a fara biya, ko kuma yadda zai shafi ma’aikatan jihohi da kananan hukumomi.
A halin da ake ciki dai, har yanzu jihohi da dama ba su fara biyan mafi karancin albashi na Naira 30,000 ba.
2- Radadin cire tallafin mai
Tinubu ya ce yana sane da wahalar da ’yan Najeriya ke ciki a sakamakon cire tallafin ma, amma duk da haka dole sai da su yi hakuri, muddin suna so kasar ta kai ga tudun mun tsira.
Ya yaba wa gwamnatin Buhari da ta gabace shi kan cire tallafin, wanda ya ce, “ya fi amfanar masu arziki a kan talakawa.
“Ganin irin karancin kudin da kasar ke ciki da makudan kudaden da tallafin ke ci, gara mun yi amfani da kudin tallafin a ingangata bangarorin ilimi da lafiya da sanar da ayyukan da za su inganta rayuwar miliyon jama’a.”
3- Salon gwamnati
Ya ce matakan da gwamnatinsa ta tsara domin kawo ci gaban kasar su ne: Tabbatar da jagornacin bisa yadda kundin tsarin mulki ya tsara.
Sauran su ne tabbatar da tsaro da zaman lafiya, sai damawa da matasa da mata sosai; na hudu, da kuma karfafa hukumomin yaki da almundahana.
Na biyar shi ne inganta tattalin arziki domin cigaban kasa, samar da ayuka, yakar talauci da kuma tabbatar da wadatuwar abinci.
4- Bangaren tsaro
Tinunu ya yaba wa jami’an tsaro bisa fadi-tashinsu na tabbatar da aminci tare da murkushe duk wasu barazanar tsaro a Najeriya.
Ya yi ta’aziyyar wadanda suka kwanta dama, sannan ya yi alkawarin inganta yayanin aikin bangaren tsaro da samar da duk abubuwan da suke bukata na horo da kayan aiki da yanayin aiki da sauransu domin su yi nasara.
5- Wutar lantarki
Shugaban kasar ya ba wa al’ummar kasar tababci samun ingantacciyar wutar lantarki domin farfado da masana’antu da kananan sana’o’i da kuma jawo masu zuba jari daga kasashen waje.
Ya ce da zarar an kammala ayyukan da ake yi a bangaren, za a ninka karfin wutar lantarkin kasar, kuma zai ba wa jihohi kwarin gwiwa su gina tashoshinsu na lantarki.
6- Samar da ayyuka
A cewarsa, gwamanti za ta dubi korafe-korafen al’umma kan yawan haraji da wasu tsare-tsare da ke tarnaki ga bangaren kasuwanci da masana’antu.
“Za mu yi iya kokari wajen ganin ’yan kasuwa na cikin gida da na kasashen waje sun shigo kuma suna samun riba.
“Za mu samar wa matasa ayyuka masu inganci, mu cika alkawarin da mukyi na samar ayyuka miliyan daya a bangaren sadarwa na zamani
“Za mu tabbatar da adalci da cancanta wajen nade-naden mukamai,” ta yadda kowane jinsi, nakasassu da matasa, sa sauran bangarorin al’ummar kasar sun samu wakilci da wani kaso a cikin gwamnati.
Ya ce bangaren zartaswa da majalisar dokoki za su hada kai wajen yin doka da kuma tsara yadda hakan zai kasance, hakazalika za a yi “dokokin da za su inganta tsarin aiki da bunkasa kananan sana’o’i da inganta rayuwar masu karamin karfi da tsofaffi.”
7- Bangaren noma
A cewarsa, za a inganta bangaren noma ta yadda manoma za su samu saukin sayar da amfanin da suka namo da daraja da kuma rage tsadar abinci ta hanyar gina ma’adanar amfanin gona domin hana lalacewarsu da nufin rage asara.
“Za a kafa cibiyoyin noma a fadn kasar nan domin bunkasa sana’ar da kara wa amfanin gona daraja; Haka ma, za a bunkasa amfani da dabarun zamani a harkar kiwo domin rage rikicin manoma da makiyaya.
Da haka ne, “Manoma za su samu kudaden shiga fiye ma’aikata, abinci ya wadata a kasa ba tare da ya yi tsada ba.”
8- Ababen more rayuwa
A cewar shugaaban kasar, zai dora daga inda gwamnatin Buhari ta tsaya a ayyukan gyaran titi da na layin dogo da ma tashoshin jiragen ruwa da na sama.
9- Tsarin kudi
Ya ce domin samar da ayyuka da bunkasa masa’anatu da zuba jari, Babban Bankin Najeriya (CBN) zai rage kudin ruwa don saukaka wa ’yan kasuwa masu karbar rancen banki.
Za kuma a yi wa tsarin canjin kudi na bai-daya garambawul da nufin hana ’yan canji yin yadda suka ga dama da farashi, wanda ke karya darajar Naira.
Game da sauya takardun kudi da takaita cirar tsabarsu da gwamnatin Buhari ta yi, Tinubu ya ce zai waiwayi lamarin.
Ya ce duk da amfanin tsarin, an tsananta wajen aiwatarwa, duba da yawan al’ummar Najeriya da ba su da asusun ajiya a banki ko da wadanda ba sa kai kudadensu banki.
Don haka za a ci gaba da amfani da tsoffi da kuma sabbin takardun N200, N500, da kuma N1,000 a tare.
10- Huldar diflomasiyya
Ya ce duba da yadda rikicin shugabancin da kuma yin juyin mulki suka zama ruwan dare a kasasehn da Najeriya ke hulda da su, musamman a Afirka, kasar ta ba da muhimmanci ga tabbatar da zaman lafiya da dorewar dimokuradiyya a nahiyar.
“Za mu ci gaba da aiki tare da kungiyar ECOWAS da AU da sauran hukumomin duniya wajen sasanta rikice-rikicen da kuma dakile masu tasowa
“Haka kuma za su ci gaba da aiki domin kawo ci gaban yankin da muke ciki,” in ji shi.