✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yanzu ’yan Afirka sun fi tsawon rai fiya da shekaru 20 da suka wuce – NSCC

Babbar Daraktar Cibiyar Kula da Dattijai ta Kasa (NSCC), Dokta Emem Omokaro ta ce yanzu haka mutane a Afirka sun fi tsawon rai fiye da…

Babbar Daraktar Cibiyar Kula da Dattijai ta Kasa (NSCC), Dokta Emem Omokaro ta ce yanzu haka mutane a Afirka sun fi tsawon rai fiye da shekaru ashirin da suka shude.

A ganawarta da manema labarai a birnin New York na Amurka bayan kammala taron ci gaban jama’a na Majalisar Dinkin Duniya karo na 61 (CSocD61), ta ce tsawon ran ya karu ne da shekaru 11.

Omakori wacce ta wakilci Najeriya a taron, ta gabatar da mukala ne kan shawarwarin masana game da bitar shirin Madrid akan Tsufa (MIPAA) a Afirka a shekarar 2018-2022,  a madadin ƙasashen Afirka 54.

Ta kuma ce A Najeriya tsawon rai ya karu da shekaru 10.6 kan yadda yake a baya, wato daga shekaru 51.7 a 1990-1995,  zuwa 62.4 a 2015-2020.

A cewarta, binciken da aka gudanar na nuna tsofaffi miliyan 110 ne ke rayuwa a Afirka, kuma yanayin girma da tsufan da ake samu a yanzu, ya sauya sosai a wasu yankunan.

“Hakan na da alaka da saurin girman da ya karu musamman a Najeriya.

“Bayanai na nuna Kudanci da Arewacin kasar sun fi yankin Tsakiya da Yammaci saurin girma, inda suke da kashi 8.3 daga kashi 6.6 a 1992.”

Ta kuma ce kasashe kamar Najeriya ba su tsaya a bunkasa manufofin kasa kan tsufa kadai ba, sun hada da kyakkyawan shirin kasa da suke aiwatarwa.

Don haka ta yi kira ga gwamnatocin sauran kasahen, da su yi koyi da kasar wajen sanya tsofaffi a tsare-tsarensu don habaka tattalin arzikin yankin.