Alhaji Aliko Dangote ya bukaci Kamfanin Mai Na Kasa na Najeriya (NNPCL) da ya zo saye matatar mansa, wadda ita ce ta biyu mafi girma a duniya.
Dangote ya yi wannan furuci na neman NNPCL ta mallake matatar tasa ne cikin takaici, kan dambarwar da ta kunno kai a kan matatar a tsakaninsa da hukumomin kula da bangaren mai na Najeriya.
Wannan dambarwa dai ta hana matatar samun adadin danyen man da take buƙata domin fara samar da tataccen man fetur a kasuwa.
A makon jiya ne Dangote ya yi zargin cewa wasu miyagu a cikin Najeriya da kasashen waje sun sha yin kokarin ganin cewa matatar tasa ba ta fara aiki ba.
- An kama su kan tono gawar dan maƙwabcinsu domin tsafi
- NAJERIYA A YAU: Alaƙar Da Ke Tsakanin Masu Haƙar Ma’adanai Da ’Yan Bindiga
Matatar Dangote ba ta da lasisi —MNDPRA
Amma daga bisani Hukumar Kula da Albarkatun Mai (MNDPRA) ta bullo tana zargin matatar Dangote da samar da man dizel mara ingancin da ake bukata idan aka kwatanta da wanda ake shigo da shi daga kasashen waje.
Babban Jami’in MNDPRA, Farouk Ahmed, ya shaida wa ’yan jarida a Fadar Shugaban Kasa cewa, a sakamakon haka, Najeriya ba za ta dogara da matatar Dangote domin samar da man da ake bukata a kasar ba.
Farouk Ahmed ya kara da cewa, hasali ma, matatar ta Dangote ba ta da lasisin fara aiki a Najeriya.
Ya kuma ƙaryata zargin da ake wa hukumar MNDPRA na neman hana wa matatar Dangote ruwa gudu, ta hanyar rashin samun danyen mai daga kamfanonin hakar mai na kasashen waje.
Martanin Dangote
Amma a wata hira ta musamman da ya yi da kafar labarai ta Premium Times, Alhaji Aliko Dangote ya ce, idan NNPCL na so, za su iya zuwa “su saye matatar daga hannuna su gudanar da ita yadda suke ganin ya fi dacewa.
“Sun ce na yi kane-kane na tare komai, alhali ba haka ba ne. Amma babu komai.
“Idan suka saye matatar daga gareni, shi ke nan sun kawo karshen wanda suke ganin ya yi musu kaka-gida,” in ji dan kasuwar.
Tasirin Matatar Dangote
A shekarar 2023 aka kaddamar da matatar Dangote mai karfin tace gangar danyen 650,000 a kullum, wadda aka gina a kan Dala biliyan 19.
Ana kuma kyautata zaton matatar za ta taimaka wajen rage matsalar mai da kuma dogaro da kasashen waje a bangaren.
Hakan zai rage asarar kashi 30% na kudaden da kasar take asara a bangaren musayar kudaden ketare domin shigo da kayayyaki.
A hiharsa da Premium Times, Aliko Dangote ya ce: “Tun shekarun 1970 ake fama da matsalar mai a kasar nan.
“Wannan matata za ta taimaka wajen magance matsalar, amma akwai mutanen da ba su so, saboda tawa ce.
“Sabosa haka a shirye nake in bar musu matatar, NNPCL ta zo ta saya akwai ta ci gaba da gudanar da ita.”
Majalisa za ta bincika
Wata majiya mai karfi ta shaida mana cewa shugaban MNDPRA zai gurfana ranar Litinin a gaban kwamitin Majalisar Wakilai domin amsa tambayoyi kan wannan lamari.
Majalisar na so ta gano ko shin da gaske gwamnati tana da hannu a makarkashiyar da Aliko Dangote ke zargi.
Kwararru a fannin tattalin arziki dai sun shawarci Gwamnatin Tarayya da hukumominta su ba da damar kafa matatun mai masu zaman kansu irin ta Dangote, domin bunkasa tattalin arzikin kasa.
Fadar shugaban kasar ta yi gum da bakinta
Aminiya ta nemi jin gaskiyar ikirarin da Farouk ya yi cewa Fadar Shugaban Kasa na goyon bayan hukumar kan dambarwarsu da Matatar Dangote.
Wakikinmu ya tuntubi Mashawarcin Shugaban Kasa kan Harkokin Yada Labarai, Bayo Onanuga, amma ya ki cewa komai.
Amma ya ba da lambar Babbar Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Makamashi, Misis Olu Verheijen.
Amma duk kokarin da muka na samun ta ya faskara, domin kuwa ba ta amsa kiran waya ba, haka kuma ba ta amsa rubutaccen sakon da muka aika mata ba.
Mun so yin amfani da damar domin jin irin matakin da shugaban kasa ya dauka ko zai dauka kan lamarin, a matsayinsa na mai rike da ofishin ministan mai.
Wannan dambarwa dai ana ganin babbar illa ce ga gwamnatin Najeriya, kasancewar wasu ’yan kasar sun fara cewa zargin ana yi wa matatar zagon kasa.
Masana kuma na ganin cewa wannan rikici zai kawo wa kasar cikas, domin zai kashe wa masu sonmsu zuba jari a kasar gwiwa.