Kungiyar kwadago ta shawarci shugaban kasa Bola Tinubu da ya yi abin da ya kamata wajen kauce wa zanga-zangar tsadar rayuwa da kunno kai a Najeriya.
Shugaban NLC, Joe Ajaero ya ce yana da muhimmanci shugaban kasa ya shawo kan lamarin ta hanyar tattaunawa da jagororin wannan zanga-zanga.
Dubban ’yan Najeriya ne suke shirin gudanar da zanga-zanga a fadin jihohi 36 a watan Agusta sakamkon tsadar rayuwa kasar.
Shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajaero, ya bukaci shugaban kasar da ya bayyana kira shugabannin zanga-zangar tare da tattaunawa da su domin su fahimci dalilan da zai sa su janye.
- Sheikh Tijjani Guruntum ya gwangwaje dalibansa da kyautar kuɗi da kayan abinci
- ’Yan ta’adda sun fara amfani da jirgi mara matuki —ONSA
- Tinubu ya mika kudurin karin albashi zuwa N70,000 ga Majalisa
Ajaero ya yi kira na musamman ga Tinubu da ya saurari kukan jama’a, inda ya kara da cewa miliyoyin ’yan Najeriya ba su ji dadin halin kuncin da kasar ke ciki.
Ya kokda da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki a halin yanzu, inda iyalai da yawa ba sa iya samun abin da za su ci a rana ba.