✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yanzu da nake shugabanci ne ya fi dacewa Kwankwaso ya dawo APC – Ganduje

Babu wanda zai ce Kwankwaso ba dan siyasa ba ne.

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce a shirye suke su karbi tsohon Gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso a jam’iyyarsu.

Ya ce kasancewar yanzu dan jiharsa ne yake shugabancin APC, babu wani lokaci da ya fi dacewa Kwankwaso ya koma jam’iyyar sama da yanzu.

Ya bayyana hakan ne yayin wata hira ta musamman da kafafen yada labarai na jihar Kano da daren Asabar, inda ya ce ya lura Kwankwason ya jima yana rara-gefen komawa APC.

A cewarsa, “Babu wanda zai ce Kwankwaso ba dan siyasa ba ne, akalla ya yi Gwamna har sau biyu, amma a karkatse, ya yi Ministan Tsaro, duk da bai ma san mene ne tsaron ba, sannan ya yi Sanata duk da bai ce komai ba a majalisa.

“Amma idan yana son dawowa APC, kofa a bude take, musamman ma yanzu da dan jiharsa ne ke shugabancinta. Ka ga ko kamun kafa zai tafi nema ba zai sha wahala ba ke nan,” in ji shi.

Da aka tambaye shi batun ba Kwankwason mukami da dan takarar Shugaban Kasa na NNPP din ya ce Shugaba Tinubu zai yi, Ganduje ya ce dama can a bakin Kwankwason aka ji maganar ba a bakin Tinubu ba.

“Gaskiya ne Tinubu ya yi alkawaein yin gwamnatin hadin kan kasa, kuma ya cika, tun da ga Nyesom Wike nan daga PDP ya sami kujerar Minista. Amma shi wancan da ya ce za a ba shi mukami, daman daga bakinsa maganar ta fito, ba daga bakin Tinubu ba,” inji Ganduje.