✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kanawa ne suka bukaci a cire sunan Maryam Shetty daga minista ba ni ba – Ganduje

Ya ce surutan kafafen sada zumunta ne suka sauya tunanin Tinubu

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce surutan da mutanen Jihar Kano suka rika yi a kafafen sada zumunta kan nadin Maryam Shetty ne suka sa Shugaban Kasa ya canza shawararsa a kan nada ta minista.

A ranar Larabar da ta gabata ce dai Shugaba Bola Tinubu ya aike da sunan Maryam Shetty da wasu mutum 18 domin nada su ministoci.

Sai dai aike wa da sunan Maryam daga jihar Kano ya janyo ce-ce-ku-ce musamman a kafafen sada zumunta a Jihar, inda kashegari Tinubu ya sanar da janye sunanta tare da maye gurbinta da Dokta Mariya Bunkure.

An dai yi ta guna-gunin cewa Ganduje, wanda tsohon Gwamnan Kano ne, ya taka muhimmiyar rawa wajen cire sunan Maryam din da kuma maye gurbinta da na Mariya, wacce tsohuwar Kwamishina ce a gwamnatinsa.

Sai dai a yayin wata tattaunawarsa da wasu kafafen yada labarai da daren Asabar, Ganduje ya ce surutan da aka rika yi ne suka canza tunanin Tinubu.

Ya ce, “Lokacin da aka bayyana sunanta, mutane sun yi ta ce-ce-ku-ce a soshiyal midiya, ka san kuma wadannan kafafen na da tasiri sosai. Sai Shugaban Kasa ya kira ni ya tambaye ni, ku kuka bayar da sunanta, na ce masa a’a.

“Sai ya tambaye ni ko na santa, na ce ban santa ba, sai ya ce to yaya aka yi aka shigar da sunanta in ba daga wajenku yake ba?

“A nan janye sunanta, inda ya nemi shawarar wacce zai maye gurbinta, tun da dole ya ce mace yake so, sai muka ba shi sunan Dokta Mariya, tun da akalla ita mun yi aiki da ita, kuma mun san kwarewarta.

“Sannan wajen zabarta, mun yi la’akari da yankin da ta fito na Kano ta Kudu, wanda ya sha korafin cewa a baya ana danne shi, ka ga yanzu mun yi adalci ke nan,” in ji shi.

Sai dai ya ce duk da haka, yana da kwarin gwiwar Shugaban Kasa ba zai bar Maryam din haka ba, zai ba ta wani muƙamin a nan gaba.