Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kammala shirye-shiryenta na daƙile tashin hankalin ko wata fitina, musamman zanga-zangar da ake shirin yi a ranar 1 ga watan Oktoba.
’Yan sanda sun tura jami’ansu zuwa wurare masu muhimmanci a faɗin jihar kuma sun yi gargaɗi mazauna Kano da su ƙaurace wa fita kan tituna domin yin zanga-zanga.
- ’Yancin Kai: Barau ya roƙi ’yan Najeriya su ƙauracewa zanga-zanga
- Harin jiragen Isra’ila ba zai kawo karancin mai ba —’Yan Houthi
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne, ya bayyana hakan a ranar ranar Litinin.
Ya ce rundunar ba za ta yarda a sake fuskantar irin tashin hankalin da aka yi a lokacin yayin zanga-zangar #EndBadGovernance ba.
“Dangane da bikin Ranar ’Yancin Kai na 1 ga watan Oktoba 2024, rundunar ta kammala dukkanin shirye-shiryen samar da isasshen tsaro kafin da kuma bayan bikin.
“Saboda haka, ina kira ga duk mazauna Jihar Kano da su haɗa kai da ’yan sanda da sauran jami’an tsaro su gudanar da bikin cikin koshin lafiya, tare da bin duk la’idojin tsaro da mutunta haƙƙin wasu.
“Haka kuma, an tura jami’an tsaro zuwa wurare masu muhimmanci domin hana kowace irin barazanar dangane da zanga-zangar da ake zaton za a yi a ranar 1 ga watan Oktoba.
“Dole ne mu fahimci cewa an samu raguwar aikata laifuka sosai,” in ji Kiyawa.
Kiyawa, ya ƙara da cewa, bisa ga umarnin Sufeta-Janar na ’Yan Sanda, Kayode Adeolu Egbetokun, rundunar ta fara haɗa kai da al’umma tare da gudanar da bincike domin daƙile laifuka.