Shugaba Bola Tinubu zai yi wa ’yan Najeriya jawabi a ranar Talata, 1 ga watan Oktoba 2024, da misalin ƙarfe 7 na safe.
Wannan sanarwa ta fito ne daga Bayo Onanuga, Mai Magana da Yawun Shugaban Ƙasa a ranar Litinin.
- Manyan makarantu sun fara yajin aikin gargaɗi a Yobe
- Ba zan yi wa harkar shari’a katsa-landan ba — Tinubu
Sanarwar ta ce “Shugaba Tinubu zai yi jawabi ga ’yan Najeriya.”
Jawabin na daga cikin shirye-shiryen bikin murnar cika shekaru 64 da samun ‘yancin kan Najeriya.
Sanarwar ta ƙara da cewa za a yaɗa jawabin a gidajen talabijin, rediyo, da sauran kafafen watsa labarai ciki har da Gidan Talabijin na Najeriya (NTA) da Gidan Rediyon Tarayya (FRCN).
Wannan shi ne karo na farko da Shugaba Tinubu zai yi wa al’ummar ƙasar nan jawabi tun bayan zanga-zangar #EndBadGovernance da ta tilasta masa yin jawabi.
Sai dai da dama daga cikin ‘yan Najeriya ba su ji daɗin jawabin da ya yi ba, domin bai ce komai game da buƙatun masu zanga-zangar ba.