Gwamna Charles Soludo na Jihar Anambra ya ce mafi rinjayen kaso na waɗanda jami’an tsaro ke kamawa da aikata laifuka tsawon shekara uku da suka gabata ’yan kabilar Ibo ne.
BBC ya ruwaito Soludo yana bayyana hakan a yayin wani taro da ’yan asalin jihar mazauna ƙetare suka gudanar a Amurka.
- Jami’an tsaro sun hallaka ’yan bindiga 30 a Katsina
- HOTUNA: Obi ya ziyarci iyalin Ɗantata don yi musu ta’aziyya
Soludo wanda tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) ne ya yi watsi da zargin da ake yi wa Fulani makiyaya na aikata satar mutane a jihar.
“Yanzu shekara uku da wata uku ke nan ina kan mulki. Idan muka kama masu laifi 100 to kashi 99 cikin 100 matasan ƙabilar Ibo ne,” a cewar gwamnan.
“Karya da farfaganda ake yaɗawa cewa Fulani ne ke aikata laifukan. Waɗannan karerayin da ake yaɗawa su suka buɗe kofa ga matasanmu shiga satar mutane saboda ta fi kawo kuɗi kan sana’arsu ta ‘Yahoo’ da safarar ƙwayoyi.”
Anambra na cikin jihohin Kudu maso Gabashin Najeriya da ’yan bindiga masu fafutikar kafa ƙasar Biafra suka dinga hana mutane fita harkokinsu duk ranar Litinin a baya domin nuna ɓacin ransu kan kamawa da kuma tsare jagoransu Nnamdi Kanu da Gwamnatin Tarayya ta yi.