✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Yahoo sun harbe jami’in EFCC har lahira a bakin aikinsa

Ganin jami'an EFCC ke da wuya sa ’Yan Yahoo ɗin suka buɗe musu wuta, suka kashe wani mai muƙamin Mataimakin Sufurtanda, suka jikkata wani da…

Masu damfara ta intanet, waɗanda aka fi sani da ’Yan Yahoo, sun karbe wani jami’in Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arziƙin Ƙasa (EFCC), har lahira a bakin aikinsa.

’Yan Yahoo sun kashe shi tare da jikkata wani abokin aikinsa ne a yayin da shi da tawagar jam’an EFCC suka kai samame a wata matattarar ɓata-garin a Jihar Anambra.

Ganin jami’an ke da wuya sa ’Yan Yahoo ɗin suka buɗe wuta, suka kashe wani mai muƙamin Mataimakin Sufurtanda, suka jikkata wani da raunin harbi a yayin da sauran jami’an suka sha da ƙyar.

Aminiya ta gano cewa wanda aka jikkata yana kwance ranga-ranga ana jinyar sa a wani asibiti, da ba a bayyana ba.

An tura jami’an na EFCC aikin a Jihar Anambra ne daga babban Ofishin Hukumar da ke Enugu.

Da yake tabbatar da faruwar hakan, kakakin ’yan sanda na Jihar Enugu, Tochukwu Ikenga, ya ce, “muna gudanar da bincike, amma wanda ake zargin ya shiga hannu kuma mun ƙwace bindigar a hannunsa.”