’Yan wasan tawagar kwallon kafar Kamaru sun bukaci a bai wa wadanda turmitsitsi ya shafa a wajen filin wasa na Olembe kudaden da aka alkawarta za a ba su sakamakon ketarawa zuwa zagaye na biyu na gasar AFCON.
’Yan wasan sun shigar da wannan bukata ce ga Shugaban Hukumar Kwallon Kafar kasar, Samuel Eto’o wanda kuma tuni ya amince kamar yadda kakakin tawagar kwallon kafar Kamarun, Serge Leopold ya sanar.
Magoya baya 8 ne suka mutu, kana 38 suka ji rauni, 7 daga cikinsu munanan raunuka, bayan turmitsitsin da ya auku a wajen filin wasa na Olembe, gabanin wasan kungiyoyin 16 na karshe tsakanin Kamaru da Comoros.
Gidan Rediyon Faransa ya ruwaito cewa, kowane dan wasan Kamaru zai karbi dala dubu 85 sakamakon kai wa matakin sili daya kwale wata zagayen ’yan 16 na gasar ta AFCON.
Haka kuma Kamaru ta sadaukar da nasarar da ta samu a kan Gambia a wasan daf da na karshe na ranar Asabar da ta gabata ga wadanda wannan iftila’i ya rutsa da su.
Aminiya ta ruwaito cewa, a Litinin da ta gabata ce turmutsitsin jama’a ya auku a wajen wani filin wasanni da ke Yaounde da ake buga gasar cin Kofin Nahiyar Afirka da ke wakana a Kamaru.
Lokacin da lamarin ya faru, Gwamnan yankin Tsakiya na Kasar Kamaru, Naseri Paul Biya ya bayyana cewa akwai yiwuwar adadin wadanda suka mutun ya karu.
Wannan turmutsitsin dai ya auku a yayin da jama’a suka rika kokawar samun damar shiga filin wasa na Olembe da ke Younde, babban birnin kasar domin kallon wasan zagayen ’yan 16 da ya gudana tsakanin Comoros da kasar ta Kamaru da ka zaman mai masaukin baki a gasar AFCON 2021.
Jaridar Wasanni ta Marca ta ruwaito mahukunta na cewa, an garzaya da akalla mutum 40 da suka jikkata zuwa asibitin Messassi wanda kuma cikinsu har da kananan yara da suka suma.
Wata malamar jinya a asibitin mai suna Olinga Prudence ta ce, “an kawo wasu da suka galabaita da ke bukatar kulawa cikin gaggawa, wanda tilas muka mika su zuwa wani babban asibitin kwararru.
Masu ruwa da tsaki a harkar tamaula sun ce mutum 50,000 ne suka yi kokarin shiga filin domin kallon wasan.
Haka kuma, bayanai sun ce filin wasan na iya daukar mutum dubu 60 ne, amma saboda matakan da mahukuntan lafiya suka gindaya na dakile yaduwar cutar Coronavirus, ba a yarda wadanda za su shiga filin ya haura kashi 80 cikin 100 na adadin da filin wasan zai iya dauka ba.
An dai fafata a zagaye na biyu na gasar duk da faruwar wannan al’amari, wanda rahotonsa bai bulla ba sai bayan an tashi daga wasan.
A wasan ne dai kasar Kamaru ta yi nasara a kan Comoros da 2-1, da hakan ya ba ta damar tsallakawa zuwa zagayen Quater Finals a gasar.