Cristiano Ronaldo na kasar Portugal, ya zama dan wasa mafi albashi a duniya bayan da kungiyarsa ta Al Nassr da ke kasar Saudiyya ta ninka masa albashinsa.
Mujallar Forbes ta ruwaito cewa karin albashin buga wasa da Al Nassr ta yi wa Ronaldo da kusan kashi 100, ya sa yanzu yana kabar sama da Naira biliyan 62.6 (Dala milian 136) a shekara.
- Daliban Najeriya da suka isa Port Sudan za su iya hawa jirgin sama
- DAGA LARABA: Yadda Iyaye Ke Kashe Wa ’Ya’yansu Aure A Arewa
Kawo yanzu dai babu wani dan wansa a duniya da albashinsa ya kai na Ronaldo, wanda a baro ya raba gari da kungiyar Manchester United ta kasar Birtaniya, ya dawo Al Nassr.
Forbes ta bayyana cewa dan wasan da ke biye Ronaldo a albashi shi ne, babban abokin hamayyarsa kuma Kyaftin din kasar Argentina, Lionel Messi na kungiyar PSG, wanda ke karbar Naira biliyan 59.8 (Dala miliyan 130) a shekara.
Dan wasa na uku shi ne Kylian Mbappe na kungiyar PSG kuma Kyaftin din kasar Farasan, wanda albashinsa Naira biliyan 55.2 (Dala miliyan 120) a shekara.
A matasyi na hudu shi ne dan wansa kwallon kwando na kungiyar Los Angeles Lakers na kasar Amurka, LeBron James, da ke karbar Naira biliyan 55 (Dala miliyan 119.5)
Sai dan wasan damben boksin na kasar Mexican, Canelo Alvarez da ke da albashin Niara biliyan 50.6 (Dala miliyan 110), a matsaiyi na biyar.