✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan uwan juna da suka kashe dan A Daidaita Sahu sun shiga hannu

Wadanda ake zargin sun ce sun kware wajen satar babura

Wasu matasa biyu ’yan uwan juna sun shiga hannu kan zargin hada baki da kisan wani direban A Daidaita Sahu sannan suka sace babur din.

Mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Ogun, SP Abimbola Oyeyemi, ya ce bayan matasan sun sassari mai A Daidaita Sahun da adda sun kashe shi, sai suka jefar da gawar a bakin rafi a yankin Ijebu-Ode ta jihar.

“Bayan samun rahoton abin da ya faru, DPO na yankin Obalende, SP Murphy Salami, ya jagoranci ’yan sanda zuwa wurin,  inda suka samu gawar mai babur din a sassare shi da adda, an kuma yi awon gaba da babur dinsa,” in ji Oyeyemi.

SP Salami ya ce bayan zurfafa bincike sun gano daya daga cikin wadanda ake zargin a yankin Ikorodu na Jihar Legas da wayar marigayin a hannunsa.

“Tsare shi da aka yi ya taimaka wajen kamo dan uwansa a yankin Ikorodu; Da aka tsananta bincike, su biyun sun amsa laifinsu,” in ji jami’in.

Ya kara da cewa, wadanda ake zargin sun shaida musu cewa su kwararru ne wajen satar babura, wanda kawo yaznu sun saci babura kimanin guda takwas.

Salami ya ce sun gano addar da aka yi amfani da ita wajen aikata kisan da kuma wayoyi guda biyu da aka sace wa marigayin.

Ya ce Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Ogun, Frank Mba, ya ba da umarnin a mika batun ga sashen binciken manyan laifuka na don zurfafa bincike.