Sojojin ’yan tawaye masu neman kafa kasar Ambazoniya daga kasar Kamaru sun halaka wani basarake da mutum 11 a garin Manga da ke kan iyakan Najeriya da Kamaru a Jihar Taraba.
Mazauna yankin sun fara kaura domin tsira da rayuwarsu ne bayan sojojin sa-kai sun mamaye garin na Manga wanda ke cikin Karamar Hukumar Takum a ranar Laraba suka yi wa mutane luguden wuta.
- Mata 11,200 aka yi wa fyade a Najeriya a 2020 —Amnesty Int’l
- Najeriya A Yau: Yadda Ake Taimakon Wanda Wuta Ta Kona
Shugaban Karamar Hukumar Takum, Mista Tikari, ya bayyana cewa an gano gawarwaki biyar daga cikin wadanda aka kashe kuma al’ummar yankin duk sun kaurace wa gidajensu.
Ya ce an tura sojoji daga barikin sojoji dake garin Takum domin kare rayukan mazauna kan iyakan Najeriya da Kamaru da a karamar hukumar.
A watan jiya ma sojojin kasar Kamaru sun afka wa wasu garuruwa uku da ke Karamar Hukumar Kurmi a jihar ta Taraba inda suka kona gidaje da wuraren kasuwanci.