Gwamnatin Burkina Faso ta ce wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan tawaye ne sun sace mata 50 a lardin Soum da ke Arewacin kasar.
Rahotanni sun ce an sace mutanen ne a ranakun 12 da 13 ga watan Janairun 2023.
- Rashin tabbas kan sadaki ya kawo tsaiko a shari’ar raba auren ’yar Ganduje
- Bayan wata 11, farashin kayayyaki ya sauka a karshen 2022 a Najeriya – NBS
Maharan da ke dauke da muggan makamai dai sun kwashe matan ne lokacin da suke tsaka da dibar wasu ’ya’yan itatuwa a kauyen Liki mai nisan kimanin kilomita 15 Arewa da garin Aribinda, da kuma a wani lardin da ke Yammacin garin.
Gwamnan yankin Sahel da ke kasar, Laftanar-Kanal Rodolphe Sorgh, ya fada a cikin wata sanarwa ranar Litinin cewa, “Tun lokacin da labarin sace su ya bayyana muka dukufa yunkurin ceto wadannan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.”
Wata majiya daga jami’an tsaron kasar ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa (AFP) cewa “Muna amfani da duk wata dama da muke da ita, ta sama da ta kasa, wajen ganin mun gano tare da ceto matan.
“Akwai jiragen yagi da ke sahwagi a sararin samaniya domin gano hanyoyin da maharan suka bi.”
Hukumomi a yankin da lamarin ya faru dai sun ce sojoji da masu taimaka musu daga fararen hula sun kai wasu hare-haren da ba su sami nasara ba a yankin.
Shi ma Shugaban Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk, a cikin wata sanarwa ranar Litinin, ya yi kira da a gaggauta sakin mutanen.