✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Yan tawaye ne suka jefa Yemen cikin mawuyacin hali –Saudiyya

Ministan Harkokin Wajen Saudiyya Adel al Jubeir ya kare matakin da kasarsa ta dauka na shiga yakin Yemen, inda ya ce ’yan tawaye ne suka…

Ministan Harkokin Wajen Saudiyya Adel al Jubeir ya kare matakin da kasarsa ta dauka na shiga yakin Yemen, inda ya ce ’yan tawaye ne suka haddasa wa kasar halin da take ciki a yanzu.

Da yake tattaunawa da BBC, al-Jubeir ya zargi ’yan Shi’a na kabilar Houthi a Yemen, da tilasta wa yara ’yan shekara 9 shiga yakin da suke yi da gwamnati, da kuma sace kayan agajin da ake kai wa fararen hula.

Jami’an Majalisar dinkin Duniya sun ce ana dora alhakin mutuwar yawancin fararen hular da ake hallakawa a yakin ne kan Saudiyya da ke jagorantar kai hare-hare ta sama.

Da yake jawabi gabanin kai wata ziyara kasar Bahrain da yarima mai jiran gado Muhammad Bin Salman zai yi, Mista Jubeir ya ce gwamnatin Saudiyya na kokarin ganin an magance matsalar masu tayar da kayar baya, da ’yan tawaye da kusan daukacin kasashen Labarawa ke fama da su a halin yanzu.

Saudiyya dai tana shan suka kan matakin shiga yakin da ake yi a Yemen, inda masu sharhi kan al’amuran Gabas ta Tsakiya ke ganin kamata ya yi ta zama mai shiga tsakani a duk lokacin da rikici ya barke a yankin kasashen Larabawan.

Tun bayan hambarar da gwamnatin Shugaba Ali Abdallah Saleh, kasar Yemen ta shiga tashin hankalin da ya faro kamar na siyasa inda daga bisani ya rikide ya zama na kabilanci.

Dubban fararen hula ne suka rasa muhallansu, yayin da wadansu suka rasa rayukansu a shekarun da aka dauka ana yaki a Yemen.

Majalisar dinkin Duniya ta nuna damuwa kan halin da fararen hula ke ciki, inda ta ce mata da kananan yara da tsofaffi ne suka fi shan wahala a kasar.