Wasu ’yan taratsi sun ba wa kamfanonin hakar mai umarnin ficewa daga Jihar Akwa Ibom nan take.
Kungiyar ’yan taratsin karkashin inuwar Unyekisong Akwa Ibom ta ce ta ba da umarnin ne saboda abin da suka kira barnar da kamfanonin suke yi a al’ummomi masu arzikin mai.
- Matsalar tsaro na barazana ga kasancewar Najeriya kasa daya – Gwamnonin Arewa
- Yadda aka bude wa budurwa wuta a gaban mahaifiyarta
Sanarwar da Shugabannin kungiyar, Dede Udofia da Ibanga Ekang, suka fitar ta ce ya zama wajibi kamfanonin sun fice daga yankin tunda ba sa amfanar al’ummomin da suke hakar mai da komin.
Sanarwar ta ce in banda kamfanonin hakar mai na ExxonMobil Savannah, duk sauran kamfanonin sun ki yin ayyukan taimakon al’ummomin yankin da suke amfana da arzikin mansu.