Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta gano ’yan takarar shugabancin ƙaramar hukuma 20 a maso ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a Jihar Kano.
Kwamandan NDLEA na Jihar Kano, Abubakar Idris Ahmad, ya ce gano su ne bayan gwajin ta’ammali da miyagun ƙwayoyi da hukumar ta yi musu.
Hukumar ta yi wa masu neman kujerar ciyaman gwjin ne gabanin zaɓen ƙananan hukumomin jihar Kano da ke tafe.
Abubakar Idris Ahmad, ya ce an gano ’yan takarar da Jam’iyyar NNPP mai mulkin jihar ta gabatar da ke shan ƙwayoyi irin su opioids, hemp benzodiazepines da nicotine.
- Ambaliya ta kashe ’yan Boko Haram a Dajin Sambisa
- Maiduguri: Ruwa ya tono gawarwaki, ana fargabar harin macizai
Amma ya ce babu macen da aka samu da shan miyagun ƙwayoyi.
Jami’in ya ci gaba da cewa za a ci gaba da yi sauran ’yan takarar gwajin ƙwayoyin kafin wa’adin da Hukumar Zaben Jihar Kano (KANSIEC) ta sanya ya cika.
A ranar 26 ga watan Oktoba, 2024 ne dai KANSIEC za ta gudanar da zaben ƙananan hukumomi 44 da ke Jihar Kano.
Shugabannin ƙananan hukumomi 44 da kansiloli 484 ne za a zaɓa a ranar.