✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan ta’addan ISWAP sun kashe makiyaya 21 a Borno

Maharan sun fille wa makiyayan kai ne da adduna

Akalla makiyaya 21 ne aka rawaito mayakan kungiyar ta’addanci ta ISWAP sun kashe a wasu hare-hare daban-daban a Jihar Borno.

Bayanai sun nuna cewa ’yan ta’addan da suka hau kan babura 17 sun kai hari tare da kashe wasu makiyaya 14 a garin Kukawa da yammacin Talata, 25 ga watan Yuli, 2023 bayan sun zarge su da kai rahotonsu ga sojoji.

A baya-bayan nan ne dai shugabannin kungiyar ISWAP suka sanya dokar hana kamun kifi da noma da kiwo a wasu yankuna bayan zargin mutanen da yi wa sojoji leken asiri a kansu.

Zagazola Makama, kwararre kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi, ya ce ba su yi harbin bindiga ba yayin da suka yi amfani da adduna cikin wajen fille kawunan da dama daga cikin makiyayan.

Bayan sun kashe makiyayan tare da sace musu dabbobi, maharan sun nufi hanyar Kukawa, Doro da Kalla, yankunan da ake zargin ’yan ta’adda da dama sun mamaye.

Sakamakon haka, a ranar 25 ga watan Yuli, da misalin karfe 11:00 na dare, ’yan ta’addan a cikin motoci kusan 7 sun tare wasu makiyaya a cikin Kukawa tare da kashe wasu karin mutane shida bayan sun gargade su da kada su kuskura su je yankin.

Wasu daga cikin wadanda harin ya rutsa da su da suka arce daga wurin sun samu nasarar gano gawarwaki hudu daga ’yan uwansu a dajin.

Hare-haren kan makiyayan da suka dauki tsawon mako guda ana yi sun tilasta musu tserewa daga Tafkin Chadi zuwa wurare mafi aminci a cikin yankin Kamaru da Nijar da kuma Chadi.