✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rasha za ta yi wa kasashen Afirka kyautar hatsi

Shugaban Rasha, Vladimir Putin ya ce kasarsa a shirye take ta fara ba wa kasashen Afirka shida kyautar hatsi.

Shugaban Rasha, Vladimir Putin ya ce kasarsa a shirye take ta fara ba wa kasashen Afirka shida kyautar hatsi.

Da yake karbar bakucin shugabannin kasashen Afirka a taron da ya kira a birnin  St Petersburg a ranar Alhamis, ya ce nan da ’yan watanni kasashen Burkina Faso, Zimbabwe, Mali, Somalia, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kuma Eritriya za su samu ton 25,000 zwau 50,000 na hatsin kowannensu.

Ya bayyana cewa kasarsa, wadda ke yaki da makwabciyarta Ukraine, za ta iya maye gurbin Ukraine wajen samar wa kasashen Afirka hatsin da suka bukata.