✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan ta’addan ISWAP 73 da iyalansu sun mika wuya ga sojoji a Borno

Sun mika wuyan ne bayan wani harin sojoji a Sambisa

Akalla ’yan ta’addar kungiyar ISWAP 73 da iyalansu sun mika wuya ga sojojin rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) a Jihar Borno.

Wannna mika wuya na ’yan ta’adda, ya biyo bayan sabbin hare-haren sojoji na  bataliya ta 222 da ke Bama a Jihar ta Borno a ranar 31 ga Mayu, 2023.

Wani kwararre a fagen yaki da ta’addanci a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya bayyana a karshen mako, a Maiduguri cewa iyalan ’yan ta’addan sun kunshi maza hudu, mata 10 da yara 28.

A cewarsa, tubabbun ’yan ta’addan ISWAP suna zaune ne a maboyar Bula Bello, Zaramari da Garno a dajin Sambisa.

“Akwai kuma maza biyu, mata bakwai da yara tara daga maboyar kauyen Ngauri, Siraja da Nbellana,” ya kara da cewa, mace daya da yara 13, sun fito ne daga kauyukan Bula Ashe, Guraba da Nemaila.

Ya kuma bayyana cewa ’yan ta’addar ISWAP tara, manyan mata biyu da yara shida suma sun mika wuya ga sojojin runduna ta 26 Task Force Brigade Garrison, Gwoza, da ke da  iyaka da Kasar Kamaru.

Hukumomin rundunar sun ce ana ci gaba da bayyana sunayen ’yan ta’addan da suka mika wuya, inda daga nan ne za a mika su ga hukumomin da suka dace domin gudanar da su yadda ya kamata.

A wani labarin kuma, sojojin bataliya ta 222 sun kashe wani dan ta’addar Boko Haram a wani sintiri na dare a yankin Waroba.

An tsara ayyukan ne domin hana masu tada kayar bayan duk wani yancin yin aiki a yankin baki daya.