✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan ta’adda suka sace yara da mata 100 a Ramadan a Zamfara

Kananan yara da mata sama da 100 ne ake zargin ’yan bindiga sun sace daga kauyukan jihohin Zamfara da Katsina.

Kananan yara da mata sama da 100 ne ake zargin ’yan bindiga sun yi garkuwa da su daga kauyukan jihohin  Zamfara da Katsina.

Rahotanni sun nuna maharan sun yi awon gaba da mutanen ne a wasu kauyuka da ke kan babbar hanyar Gusau zuwa Funtua da ke kan iyakar jihohin Zamfara da Katsina.

Wani mazaunin kauyen Wanzamai da ke Jihar Zamfara, Sani Wanzamai, ya shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun sace akalla kananan yara 80 daga kauyen da wasu akalla mutum 20 daga kauyen Kucheri a harin.

Sani Wanzamai ya ce ’yan bindigar sun kuma sace wasu mutane daga kauyen Yankara daga Jihar Katsina a yayin harin na ranar Alhamis, 15 ga watan Ramadan, 1444 Hijiriyya.

Aminiya ta ruwaito cewa kauyen na Wanzamai da ke Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara ya sha fama da hare-haren ’yan bindiga a kwanakin baya.

A cewar Sani Wanzamai, “An yi garkuwa da yaran ne a bayan sun neman icen girki a cikin daji; su kuma manyan, wadanda har da mata a cikinsu, an dauke su ne daga gonaki da suka je aiki saboda karatowar damina.

“Babu zato, babu tsammani ’yan bindigar suka ritsa su, suka yi awon gaba da su ta cikin daji.

“Har yanzu masu garkuwa da su ba su kira ba, kuma an yi kira wayoyin manya daga cikin wadanda aka sacen amma babu wanda aka samu ta shiga.”

Zuwa lokacin da aka turo wannan rahoton, wakilinmu bai jin samu ta bakin kakakin ’yan sandan Jihar Zamfara ba, CSP Muhammad Shehu saboda wayar jami’in tana kashe.