Gwamnatin Zamfara ta tabbatar cewa ’yan ta’adda sun yi garkuwa da daliban Jami’ar Tarayya ta Gusau da ke jihar su 35 a gidajen kwanansu.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato wani jami’in gwamnatin jihar yana tabbatar da sace daliban a wasu uku na kwanan dalibai kafin asubahin ranar Juma’a.
- Jama’ar gari sun kashe ’yan ta’adda 21 a Kebbi
- ’Yan sanda sun cafke ’yan bindiga ɗauke da makamin roka a Yobe
Wannan shi ne adadi mafi yawa na dalibai da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a lokaci guda a bana.
Wata majiya ta ce maharan sun yi musayar wuta da sojoji, amma duk da haka sun tafi da daliban da suka sace.
Amma rundunar sojin da ke jihar ta bayyana cewa ta yi nasarar ceto shida daga cikin daliban, ta kuma kashe wasu daga cikin maharan a musayar wuta.
A jihar ce kuma ’yan bindiga suka yi garkuwa da masu yi wa kasa hidima takwas a hanyarsu ta zuwa wurin aikinsu a Jihar Sakkwato, kafin daga bisani daya daga cikinsu ya kubuta.
Wasu dalibai da mazauna unguwar Sabon Gida da ke daura da jami’ar, inda akwa kwashe daliban, sun bayyana cewa yawancin daliban da aka sace mata ne.
Wani dan unguwar ya ce da misalin karfe 3 na dare ne maharan suka shigo suna harbi babu kakkautawa, “suka shiga gidaje uku na kwanan dalibai, suka tisa keyar daukacin daliban da suka samu.
“Ba za a iya tantance yawan wadanda aka sace ba tukunsa, saboda gidajen kwanan dalibai uku suka shiga suka kwashe mutanen ciki.”
Zuwa yanzu dai hukumomin Jami’ar Tarayya ta Gusau ko hukumomin tsaro a jihar ba su ce komai game da lamarin ba tukuna.
Jihar Zamfara, daya daga cikin jihohin da suka fi fama da hare-haren ’yan bindiga a Najeriya ta sha fama da sace dalibai masu yawa a lokaci guda.
A lokuta da dama, ’yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai masu yawa a lokaci guda daga kanana da manyan makarantu da ke sassan jihar.