Mazuana Karamar Hukumar Shiroro a Jihar Neja sun koka da cewa ’yan ta’adda da ’yan fashin daji sun mayar da su bayi a gonakinsu.
Sun bayyana cewa ’yan bindiga sun mayar da ’yan aiki a gonakinsu, kuma a bana kawai wani shugaban ’yan ta’adda ya karɓe musu buhuna 20 na waken soya da suka noma a kauyen Allawa da kewaye da ke kusa da su.
Sakataren Hadaddiyar Kungiyar Al’ummar Shiroro, Sa’idu Salihu, ya jaddada bukatar dawo da sojojin domin samar da tsaro a yankin.
Sa’idu ya shaida wa wani taron gaggawa a Mina, fadar jihar cewa tun da aka janye sojojin watanni uku da suka gabata ’yan ta’adda suka dawo addabar mazauna yankin su ci gaba da harkokinsu na noma.
- Sabon albashi: Majalisar Kano ta amince da ƙarin kasafin N99bn
- Naman direba ’yan ta’adda suka ba karnukansu —Dokta Bashir
Ya bayyana cewa dawowar sojojin zai ba mutanen da suka yi gudun hijira damar su dawo gidajensu su ci gaba da harkokinsu na noma.
Don haka ya roki gwamnatin jihar da ta tarayya da su kara hada kai a bangaren tsaro da samar wa ’yan banga da kayan aiki domin kare al’ummomin yankunan.
Haka kuma ya roki Gwamantin Tarayya da ta jihar su biya diyya ga wadanda ’yan bindiga suka lalata wa gidaje da gonaki da sauran kadarori bayan janye sojoji daga yankin.
A cewar Sa’idu, ya ce ’yan bindigar sun gayyaci al’ummaomin yankin su tattauna domin su dawo garuruwan nasu.
Amma ya ce har yanzu gwamnatocin jihar da tarayya ba su amsa tayin ba.
A nasa bangaren, Abdullah Suleiman Erena ya bayyana cewa matsalar tsaron da ke addabar gundumomin da ke yankin Lakpma sun hada da mayaƙan Boko Haram, ISWAP, Ansaru baya ga ’yan fashin daji.
Ya bayyana cewa kungiyoyin sun fara yin ƙarfi a yankin na Lakpma, wanda idan ba a yi saurin magancewa ba.