✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan ta’adda sun kashe soja da fasinjoji 5 a Borno

Sanata Ndume ya ce kashe-kashen da ake yi a yankin Goza ya zama ruwan dare a ‘yan kwanakin nan.

Wasu ‘yan ta’adda da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne sun yi wa ayarin motocin da jami’an tsaro ke rakiya a kan hanyar Gwoza zuwa Limankara zuwa Uvaha kwanton bauna, inda suka kashe soja daya da fararen hula uku.

Haka kuma an kona wasu motocin haya guda biyar ciki har da wata motar sintiri ta jami’an tsaro, yayin da kawo yanzu fasinjoji da dama ba a ji duriyarsu ba.

Majiyoyi daga jami’an tsaro da mazauna sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5 na yamma, a lokacin da sojoji da ‘yan sa-kai ke bai wa fasinjoji kariya da ke tafiye-tafiye zuwa Karamar Hukumar Gwoza da Karamar Hukumar Askira-Uba da ke Jihar Borno da kuma sauran yankunan Arewacin Jihar Adamawa.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, wasu fasinjoji mata da suka tsallake rijiya da baya sun kubuta bayan ’yan ta’addan sun yi awon gaba da su a lokacin aukuwar harin.

Kazalika, wakilin Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume, ya tabbatar da faruwar lamarin da cewa harin ya auku ne a Yammacin ranar Asabar.

Ya ce kashe-kashen da ake yi a yankin Goza ya zama ruwan dare a ‘yan kwanakin nan.

“A kullum abin nan yana faruwa, don haka muna kira ga sojoji da su kai wannan yaki zuwa inda ‘yan ta’addan suke, domin duk mun san inda suke.

“Yanzu manoma na fargabar zuwa girbi gonakinsu, don haka lokaci ya yi da ya kamata su hada karfi da karfe da sojoji don ganin an samu aminci a yankin,” inji shi.

%d bloggers like this: