Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun hallaka akalla mutane 11 masu saran itace a Karamar Hukumar Damboa da ke Jihar Borno.
Rahotanni sun ce mayakan sun tare masu yin itacen ne a yammacin jiya Litinin a kauyen Damboa Iga da ke kusa da Bale, inda suka hallaka wasu daga cikin su.
- Jerin shugabannin gudanarwar NNPCL 9 da Tinubu ya naɗa
- Abin da ya kawo cikas a sulhun ECOWAS da sojin Nijar — Yusuf Tuggar
Wata majiya daga jami’an sa kai da ke aiki a yankin, ta ce an samu gawarwakin mutane 6 daga cikin wadanda ke aiki a wurin, bayan an daddatsa sassan jikinsu, kuma har anyi jana’izarsu kamar yadda addinin Islama ya tanada, yayin da 5 kuma suka bata.
Sai dai wata majiya da ta tsallake rijiya da baya, ta ce mutanen suna aiki ne a wajen da suke saran itace suna mayar da shi gawayi, lokacin da mayakan haye a kan rakuma suka afka musu, bayan sun musu kawanya.
Majiyar ta shaida wa wakilinmu cewar, lokacin da take gudu, mutanen sun bi ta, amma da yake ta fi su sanin yanayin hanyar, sai ta tsere musu.
Majiyar ta ce daga nan ta garzaya ta shaida wa jama’ar gari, inda suka yi gangami zuwa wurin, amma sai suka tarar da gawarwakin wadannan mutane guda 6 da aka daddatsa su, yayin da a yau Talata aka samu karin gawarwaki 5 na mutanen da suka bata.
Rahotanni sun ce sojoji na can suna sintiri a yankin.