Wasu ’yan ta’adda da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne sun kashe wani jami’in dan sanda Sufeta Luka a gonarsa da ke garin Bama a Jihar Borno.
Wakiinmu ya ruwaito cewa, azal din ta afka wa jami’in wanda ke aiki da bangaren kwantar da tarzoma MOPOL 53 yayin da yake aiki a wata gonarsa da ke rukunin gidajen Mohammed Indimi a garin Bama.
- Kare rayuka da mutunta ayyukan jin kai a Gaza ya zama wajibi — MDD
- Kotu ta daure ’yan daudun da suka yi shigar mata da rawa a Kano
Bayanai sun ce an kashe Sufeta Luka ne da safiyar Litinin 30 ga Oktoba, yayin da ’yan ta’addan suka yi masa kwanton bauna kan wata itaciya a gonarsa.
Aminiya ta ruwaito cewa, ’yan ta’addan sun dauke bindigar Sufeta Luka, sannan suka tube masa riga, daga bisani kuma suka harbe shi murus.
Zagazola Makama, kwararre mai sharhi kan yaki da ta da kayar baya a yankin Tafkin Chadi, ya ce lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da jami’an ‘yan sanda da dama a yankin suka rungumi aikin noma a matsayin wata hanya ta samun karin abin dogaro da kai.
Makama ya ce wannan shi ne dalilin da ’yan ta’adda suka bullo da wannan hanya ta kai wa jami’an ’yan sanda hari, musamman domin dibar kayayyakin su na ’ya’yan sarki wato kaki da kuma bindigoginsu.
Harin da aka kai wa Sufeta Luka shi ne na biyu a cikin wata guda da aka kai irin wannan hari kan jami’an ‘yan sanda a yankin.
Ana iya tuna cewa, a farkon wannan wata na Oktoba ne wasu ’yan ta’adda suka kashe wani jami’in dan sanda yayin da yake aiki a gonarsa a jihar.