✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan ta’adda sun kai hari caji ofis a Anambra

Maharan sun kashe jami'in ɗan sanda a yayin harin.

Wasu ’yan ta’adda sun kai hari ofishin ‘yan sanda na Oba da ke Ƙaramar Hukumar Idemili ta Kudu a Jihar Anambra.

A yayin harin, sun kashe wani jamin ɗan sanda tare da jikkata wasu da dama.

Wata majiya ta bayyana cewa maharan sun kuma kai hari yankin Oba.

Ko da yake ba a san dalilin kai harin ba, amma, kamar yadda hukumomi suka bayyana a jihar.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce an kafa rundunar tsaro ta haɗin gwiwa da ta haɗa da Sojoji, jami’an tsaron Sibil Difens da sauran hukumomin tsaro, wanda suke ƙoƙarin tabbatar da tsaro a yankin.

A cewarsa, waɗanda ake zargin ’yan aware ne, sun yi ta harbi tare da jefa abubuwa masu fashewa, wanda ya ƙone wasu ofisoshi da cibiyoyi a yankin.

Sai dai wani jamin ɗan sanda ya rasa ransa a yayin harin.

An kashe wutar da ta tashi tare da taimakon sauran jami’an ’yan sanda da hukumomi.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Nnaghe Obono Itam, ya yi Allah-wadai da harin.

Ya kuma yi alƙawarin kamo waɗanda ke da alhakin kai mummunan harin domin a gurfanar da su a kotu.