Rikicin da ya barke tsakanin bangaren Bakoura Buduma na Boko Haram da kungiyar ISWAP ya yi sanadin kashe ’yan ta’adda sama da 100 a kusa da Marte da ke Jihar Borno.
Rahotanni sun nuna cewa fadan wanda ya fara da misalin karfe 12:00 na daren Asabar, ya ci gaba da gudana har zuwa ranar Lahadi a wani wurin da ake kira Bakuram da ke gabar Tafkin Chadi.
Zagazola Makama, kwararren masanin nan kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi ya fahimci cewa kungiyar ISWAP na daukar fansa ne a kan sace mayakanta 60 da kwamandoji uku da kungiyar Boko Haram ta yi.
Arangamar ta baya-bayan nan, a cewar majiyoyi, ta samu jagorancin wani mai suna Abou Idris, tsohon shugaban sashen ayyuka na kungiyar Boko Haram da kuma Bakoura wanda ya bar su zuwa ISWAP.
Majiyar ta ce an samu asarar rayuka daga bangarorin biyu amma kungiyar ta ISWAP ta fi kashe wa ’yan ta’addan na Boko Haram da daman gaske.
“Yayin da muke magana a yanzu haka, ana ci gaba da gwabzawa tare da kashe ’yan ta’adda sama da 100 daga bangarorin biyu,” in ji majiyar.
A ’yan kwanakin nan dai ana yawan samun taho-mu-gama tsakanin kungiyoyin ’yan ta’addan biyu.
Hakan dai ya kan kai ga tafka asarar rayuka da dama.