Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Ƙasa (NCTC) ta bayyana yadda ƙungiyoyin ’yan ta’adda suke amfani da ƙananan ’yan mata wajen kai harin ƙunar bakin wake tare da yin lalata da su a matsayin bayi a sassa daban-daban na kasar.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta nemi kafa asusun tallafa wa waɗanda suka kuɓutar da ayyukan kungiyoyin ta’addanci da msau tsattsauran ra’ayi daga matsalolin da suke fama da su.
Ta bayyana cewa hakan zai taimaka wajen ƙarfafawa da tallafawa waɗanda abin ya shafa da waɗanda suka tsira.
Ko’odinetan cibiyar na ƙasa Manjo-Janar Adamu Laka ne ya bayyana hakan a Abuja a wajen ƙaddamar da wani shiri na taimakon fasaha kan ingantawa da tallafa wa haƙƙi da buƙatun waɗanda ta’addancin ya shafa ta hanyar aiwatar da tanadin tsarin doka.