✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan ta’adda 129,417 sun miƙa wuya cikin wata shida — Janar Musa

An bayyana cewa alƙaluman da aka fitar sun haɗa da adadin mayaƙa 30,426, mata 36,774, da yara 62,265.

Babban Hafsan Tsaron Nijeri, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa ’yan ta’addan Boko Haram 129,417 tare da iyalansu sun miƙa wuya ga jami’an tsaro tsakanin 10 ga watan Yuli zuwa 9 ga Disamba, 2024.

Babban Hafsan ya bayyana hakan ne a taron tsaro na Afirka karo na 18 da ake gudanarwa a birnin Doha na ƙasar Qatar wanda wakilinmu ya rubuto daga cikin manhajar zoom.

Taron, mai taken: “Matakan haɓaka jagorancin jama’a don haɓaka zaman lafiya da tsaro,” Mista Patrick Agbambu na cibiyar Security Watch Africa Initiative ne ya shirya. Ya samu halartar mahalarta daga Nijeriya da ƙasashen Guinea Bissau da Gambia da Afirka ta Kudu da Kenya da Ƙatar.

Janar Musa a jawabinsa ya bayyana cewa alƙaluman da aka fitar sun haɗa da adadin mayaƙa 30,426, mata 36,774, da yara 62,265.

A cewarsa, wannan nasara ta nuna ci gaban da ake samu wajen samun zaman lafiya a tsakanin al’umma da ke bunƙasa zamantakewa da tattalin arziki a Nijeriya.

“Alaƙar da ke tsakanin ci gaban tattalin arzikin jama’a da tsaro na ƙasa ya danganta ‘yan ta’addan da suke miƙa wuya ga sojojin da ke da alaƙa da haɗin gwiwar ƙungiyoyi,”.

Ya yi nuni da cewa, wannan dabara ba kawai ta daidaita unguwanni ba ne, har ma ta samar da yanayi mai kyau ga ci gaban zamantakewa da tattalin arziki.

“Sakamakon ci gaban miƙa wuya akai-akai yana nuna tasiri mai kyau na tsarin mu,” in ji Janar Musa.

“Mun samu gagarumin ci gaba wajen samar da zaman lafiya da ke tabbatar da ingantaccen yanayin zamantakewa da tattalin arzikin ‘yan ƙasa. Yayin da ƙalubale ke ci gaba da wanzuwa, ba mu kasance kamar a yanayin watan Yunin 2023, “in ji shi.