Mabiya akidar Shi’a sun gudanar da zanga-zangar neman gwamnati ta saki shugabansu na Najeriya Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa Zeenatuddin, da ke tsare.
Maza da mata da kananan yara ’yan kungiyar IMN da ke zanga-zangar sun yi tattaki a kan titin Kano Road da ke garin Kaduna ne domin tuna zagayowar arangama tsakanin ’yan Shi’a da sojoji a Zaria a shekara biyar da suka gabata.
Mutanen dauke da kwalaye na kira ga gwamnati da ta saki shugaban nasu da matar tasa ba tare da wani sharadi ba.
- Kungiyoyin Arewa sun janye zanga-zanga saboda rikici
- Ana zanga-zanga a Kano bayan ’yan sanda sun kashe matashi
- Dattawan Arewa sun yi tir da masu goyon bayan hafsoshin tsaro
“Tun bayan zubar da jinin da sojoji suka yi a Zariya a watan Disamban 2015 muke kiran ’yan kasa da su fahimci cewa zaluntar mutum daya zalunci ne ga kowa, amma har yanzu hakarmu ba ta cimma ruwa ba”, inji jagoran zanga-zangar, Sheikh Aliyu Tirmizi.
“Yawancin mutane, duk da fin karfin da sojoji suka nuna wa Sheikh Zakzaky da mabiyansa, sun kasa yin tir da abin, suka yi shiru saboda abin da sojojin suka yi bai shafe su ba”, inji shi.
Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta saki Zakzaky ba tare da wani sharadi ba domin ya samu kula da lafiyarsa.