✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Shi’a sun halarci ibadar Kirsimeti a coci a Zariya

Jagoran ’yan Shi'a da suka halarci ibadar ya ce sun dauki Kirsimeti a matsayin ranar gudanar da bukukuwa da abota da kuma hadin kai

Mabiya akidar Shi’a sun halarci ibadar Kirsimeti tare da Kiristoci a Cocin St. Joseph Catholic da ke Samaru, Zariya a ranar Litinin. 

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito jagoran ’yan Shi’a da suka halarci ibadar,  Farfesa Isah-Hasasn Mshelgaru, yana cewa hakan zai kyautata dangantaka da kara zaman lafiya a tsakanin kungiyoyin addinan biyu.

Farfesa Isah-Hassan Mshelgaru, ya ce mabiya akidar Shi’a sun dauki Kirsimeti a matsayin ranar murna da kulla abota da kuma hadin kai.

A cewarsa, manufarsu ta taya Kiristoci murnar Kirsimeti ita ce farfado da burin samun hadin kai a tsakanin Musulmi da Kiristoci da ma mabiya wasu addinina.

Mshelgaru ya ce a matsayin Musulunci da Kiristanci na masu mabiya mafiya yawa a Najeriya, “idan sauran addinan suka hada kai da su, za a samu hadin kai a kasar.’’

Ya bayyana cewa Shi’a ta fara kai ziayra a coci-coci ne sama da shekaru 25 da suka gabata, kuma tun daga lokacin ake kara samun fahimtar juna tsakaninsu.

“Ziyarar ta rage kallon hadarin kaji tsakanin bangarorin biyu. Kiristoci suna maraba da mu kuma tare muke shawo kan wasu matsalolin ko tattauna wasu lamurran.

“Kai wa juna ziyara akai-akai ta samar da fahimta da daidaito a tsakanin bangarorin,’’ in ji shi.

Tun da farko, limamin cocin, Rabaran Isak Augustine, ya yaba da ziyarar da mabiya akidar Shi’ar suka kai musu, sannan ya yi kira da su yawaita yin hakan domin karfafa alaka da hadin kai a tsakanin bangarorin.

Daga nan sai ya yi addu’ar samun saukin matsalar tattalin arziki da matsin rayuwa da suka yi wa Najeriya katutu.

Shugabannin bangarorin biyu sun yi musayar kyaututtuka a yayin ziyarar ta ibadar Kirsimeti.