✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Faɗa da Buratai: Matan ’yan Shi’a sun yi zanga-zanga a Kaduna

Matan ’yan Shi’an da suka mutu a faɗa da sojoji a Zariya a lokacin Buratai sun bayyana cewa suna cikin ƙuncin rayuwa a tsawon shekarun…

Matan ’yan Shi’a da sojoji suka kashe a Zariya shekara tara da suka gabata sun gudanar da zanga-zanga a Kaduna.

A ranar 12 ga watan Disamba shekarar 2015 ne sojoji suka kashe ’yan Shi’a da dama a yayin wata arangama a Zariya bayan ’yan Shu’an masu tattakin Maulidi sun tare hanya tare da nuna yarda da hana Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Nijeriya, Laftanar-Janar Yusuf Buratai, da ayarin motocinsa wucewa.

Matan ’yan Shi’an da suka gamu da ajalinsu a wannan arangama sun bayyana cewa suna cikin ƙuncin rayuwa a tsawon shekarun da suka yi bayan rasuwar mazajen nasu.

Sun bayyana cewa matsin rayuwar da aka shiga a Nijeriya ta ƙara tsananin da suke ciki.

Wata daga cikin matan da ta nemi a ɓoye sunanta ta ce, “mijina yana cikin waɗanda sojoji suka kashe a ranar ba bisa haƙƙi ba, kuma tun lokacin ni ke fama da kula da ɗawainiyar ’ya’yana”

Wanda ya shirya gangamin, Muhammad Abubakar Abdullahi, ya ce sun tsara shi domin tunawa da mamatan tare da nema wa iyalansu taimako da tausayawa. Ya ce da farko sun tsara yin abin a watan Disamban 2024, amma daga bisani suka ɗage shi zuwa Janairu 2025.