Aranar Asabar da ta gabata ce wadansu matasa ’yan Sara-Suka da ake kira da ’Yan Shara a Kaduna suka dirar wa Unguwar Kwaru da ke Badarawa a karamar Hukumar Kaduna ta Arewa, inda suka datse hannun wani tsohon soja.
Tsohon sojan mai suna Sani Abdullahi magidanci ne mai ’ya’ya biyu, kuma yanzu haka yana kwance a Asibitin Barau Dikko da ke Kaduna yana jinya. Matasan wadanda suka dade suna addabar al’ummar birnin Kaduna, sun isa Unguwar Kwaru ne da misalin karfe 8:30 na daren ranar.
Rahotannin daga unguwar sun ce Sani ya fito ne daga cikin gidansu domin ya saya wa iyalinsa abin karin kumallo da safe, inda matasan suka far masa. Aminiya ta samu labarin cewa matasan rike da miyagun makamai da suka hada da wukake da adduna da sauransu, sukan yi wa unguwa dirar mikiya ne su sari duk wanda suka tarar a kan hanya da sunan suna shara.
Wakilinmu ya ziyarci Asibitin Barau Dikko inda Sani yake jinya, kuma ya bayyana masa cewa matasan sun sare shi da farko a fuska. “Ban san me ke faruwa ba kawai na gan su da yawa kusan su ashirin zuwa hamsin rike da makamai. Kafin in farga sai kawai na ji saukar wuka a fuskata. Da suka sake dagawa da nufin sake sara ta sai na tare da hannu wanda hakan ya sa suka guntule min hannun take,” inji shi.
Ya nuna wa wakilinmu inda suka sare shi a kafada bayan gutsire masa hannun dama. Sannan ya ce “Babu wata rigima da ta taba hada ni da su, kasuwancina kawai nake yi.”
Wani makwabcin Sani wanda bai bayyana sunansa ba, ya shaida wa Aminiya cewa a washegarin ranar da abin ya faru al’ummar Kwarun sun garzaya ofishin ’yan sanda, inda suka nuna rashin jin dadinsu game da abubuwan da suke faruwa ba tare da daukar mataki ba.
Da Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, ASP Muktar Aliyu ya tabbatar da cewa sun kama matasa 23 daga cikin’yan sharar da suka kai farmaki Unguwar Kawo. Ya ce ’yan sanda na ci gaba da kokari wajen dakile ayyukan ta’addaci a cikin al’umma.