✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan acaba sun yi wa mai fura fyaɗe Abuja

Abokan su biyu sun yi wa Bafulatanar fyade ne da tsakar rana bayan sun yaudare ta cewa za su sayi fura a wajen ta

Jami’an tsaron sa kai sun kama wasu abokai biyu masu sana’ar  acaba, bisa zargin yin fyaɗe ga wata Bafulatana mai tallar fura da nono a Yankin Babban Birnin Tarayya Abuja.

Wani jami’in tsaron sa kai, Usman Dantala, ya ce abokan biyu sun yi wa Bafulatanar fyade ne da tsakar rana a yankin Ikwa da ke Ƙaramar Hukumar Gwagwalada.

Ya bayyana cewa ranar Asabar da misalin karfe 2:12 na rana ne abokan biyu suka yaudari mai faurar ’yar kimanin shekaru 19 zuwa daƙin wani abokinsu inda suka yi mata fyade.

Jami’in ya ce, sun kira Bafulatanar ne da cewa za ta sayar musu da nono a gidan wani abokinsu. A can ne suka yaudare ta shiga daƙin suka kuma yi mata fyade.

Dantala ya ce wani maƙwabci ne ya ji hayaniya daga daƙin ta tagarsa, wanda hakan ya sa fita ya sanar da jama’a.

“Nan take makwabcin ya sanar da sauran mutane, waɗanda suka ruga zuwa daƙin, inda suka samu mai furar tana kuka a tuɓe, yayin da ɗaya daga cikin samarin ya tsere.”

Ya ce jami’an sun kama ɗayan wanda ake zargin, wanda kuma ya kai su wata daba inda suka kama ɗayan ma.

Daga baya jami’an sun kai mai furar asibiti, inda aka tabbatar da cewa an yi lalata da ita; aka miƙa waɗanda ake zargin ga ’yan sanda.

Kakakin ’yan sanda ta Abuja, SP Josephine Adeh, ba ta samu damar yin tsokaci kan wannan lamari ba.