✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sandan sun gano inda ake daure mutane a wata coci a Legas  

A jiya Alhamis rundunar ‘yan sandan Legas ta gano wata coci da ake tsare da wasu daurarrun mutane su 15 da aka sanya masu mari…

A jiya Alhamis rundunar ‘yan sandan Legas ta gano wata coci da ake tsare da wasu daurarrun mutane su 15 da aka sanya masu mari a unguwar Lafiya da ke yankin Ijegun Isheri a jihar Legas.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Legas DSP Bala Elkana, ya shaida wa Aminiya cewa Rundunar ‘yan sandan ta kame babban faston cocin da karin wasu mutum 10 da ake zargi da hannun a gudanar da al’amuran cocin, ya ce an kubutar da daurarrun su 15 wadanda suka hadar da maza da mata masu shekaru 19 zuwa 59, ” wasu daga cikin daurarrun iyayen su ko ‘yan uwansu ne suka kai su cocin domin nema masu maganin da suka hadar da na tabin hankali da sauran cututtuka.” In ji shi.

Babban faston cocin mai shekaru 58 mai suna Sunday Joseph Ojo, ya shaida cewa yana sanya mutanen a mari ne domin hana su guduwa daga cocin, ya ce ya kwashe sama da shekara 33 yana aikin kulawa da daurarrun wadanda yake masu magani.

DSP Bala Elkana, ya kara da cewa rundunar ‘yan sandan da sauran hukumomin da abin ya shafa na aikin kulawa da lafiyar daurarrun da kuma samar masu matsuguni ingantacce.