A ranar Alhamis Babbar Kotun Jihar Kano ta sake zaman sauraren shari’ar daukaka karar da Abduljabbar Kabara ke kalubalantar hukuncin Babbar Kotun Musulunci da ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Sai dai a zaman kotun ba a ga mai kara Abduljabbar Kabara ko kuma lauyansa ba.
Lauyan gwamnati, Barista Bashir Saleh, ya mika rokonsu a gaban kotun na neman ta fadada musu lokaci don yin suka ga rokon da masu kara suka yi.
Kotun karkashin jagorancin Masu Shari’a Nasiru Saminu da Aisha Mahmood, ta amince da rokon lauyoyin gwamnati inda daga bisani ta dage shari’ar zuwa ranar 14 ga watan Mayu, 2024.
Idan za a iya tunawa Abduljabbar Kabara ya mika wa kotun rokonsa guda biyu, inda yake kalubalantar kundin shari’ar da aka yi masa a kotun kasa, cewa ba cikakke ba ne.
Haka kuma Abduljabbar ya yi zargin cewa a cikin kundin shari’ar akwai kwange na wata sadara.