✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan Sandan Legas sun saki ‘yan cirani 123 da jami’an tsaro suka tsare

Yau Asabar da yamma ne rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta saki mutanen nan ‘yan cirani 123 da rundunar tsaron task fos ta Legas ta…

Yau Asabar da yamma ne rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta saki mutanen nan ‘yan cirani 123 da rundunar tsaron task fos ta Legas ta kame a safiyar jiya Juma’a .

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar DSP Bala Elkana ya aike wa Aminiya.

DSP Bala, ya shaida cewa rundunar ‘yan sanda tayi bincike akan mutanen ta kuma gamsu da cewa ba masu laifi bane hasali ma akwai da yawan su da ke zaune tare da iyalan su a Legas inda suke kananan sana’a wasun su kuma zuwan su ke nan a karon farko, ya ce an sallame su sun tafi inda suka nufa tun da fari.

A jiya Juma’a ne rundunar tsaro ta Legas tas fos tare da taimakon shugaban karamar hukumar Agege Alhaji Ganiyu Kola Egunjobi, suka tsare motar tirela dauke da ‘yan cirani su 123 daga jihar Jigawa tare da baburan acavar su 48 bayan da wasu jama’ar yankin suka yi zargin ko batagari ne.

Kamen ya janyo cece-kuce a kafafan zumunta na zamani inda jama’a da dama suka yi ta nuna rashin jindadin su game da lamarin.